ROKO GA GWAMNAN KATSINA: KAR A RUSA TSOHON GININ TSB

0

ROKO GA GWAMNAN KATSINA:

KAR A RUSA TSOHON GININ TSB

….Wasika daga masu kishin kayan tarihi

Daga Abubakar Abdullahi
@Katsina City News

Wata kungiya mai suna Association For Better Katsina State, sun rubuta wata wasika zuwa ga mai girma Gwamna Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, inda suke rokon sa da kar ya bari a rusa tsohon ginin Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Katsina, wanda yanzu Hukumar daukar Malaman makarantar gaba da Firamare ke ciki.

Wasikar mai shafuka biyu da sa hannun Shugaba da Sakataren Kungiyar, wadda suka bai wa jaridun Katsina City News kwafi.

A wasikar sun ce, sun san mai girma Gwamnan Katsina mutum ne mai sauraren koken jama’a da ra’ayinsu da kuma amincewa da bukatarsu.

Kungiyar ta ce ginin da ake so rusawa wani a cikinsu ya fi shekaru 100, kuma yana tafiya ne da tarihin Katsina da ci gabanta.

“Yanzu duniya tana canzawa, wanda ake killace da kara kula da duk wani gini na tarihi don masu yawon bude ido ne da kuma tuna tarihi, haka yake faruwa a kasashen Gabas da Yammacin duniya”, in ji su.

Kungiyar ta ce wasu kasashe har sun fara doka ta hana rusa duk wani gini da ya haura shekaru 100.

See also  Shahararren Malamin Addinin Musulunci Sheikh Giro Argungu Ya Zubar Da Hawaye Lokacin Dayake Hudubar Juma'a

Suka kara da cewa, wannan waje mallakar gwamnati tun zamanin Sarki Katsina Muhammad Dikko yake, kuma ya taka rawa sosai wajen ci gaba da habaka tarihi a Katsina.

Kungiyar suka ce a shekarar 2013, Shugaban Kasa Goodluk Jonathan, ya yi kokarin canza sunan Jami’ar Legas zuwa suna Jami’ar Abiola, amma al’ummar Legas baki daya suka tashi suka ce canza sunan zai taba tarihin Legas, don haka a bar Jami’ar da sunanta. Haka kuma aka yi.

Kungiyar ta ce: “Mun tabbata an yi wa mai girma Gwamna Katsina rufa-rufa ne, ba a yi la’akari da abubuwa da yawa wajen neman daukar matakin ba wani dan kasuwa don ya mallaka wa kansa da iyalinsa wannan wuri mai tarihi”.

Kungiyar ta ce in don kudi ne, a shirye suke su samo kudi wajen kungiyoyin duniya masu kula da gine-ginen tarihi don mayar wa mai Green House in har an amshi kudinsa.

Kungiyar ta ce: “Tarihi zai rubuta sunanka da ruwan tawadar Zinare in har ka hana rusa wadannan gine-ginen”.

Kungiyar ta ce tana da tabbacin za a duba kokenta, kuma za a ji ra’ayin al umma.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here