RUSA MA AIKATAR WATSA LABARAI Ba wanda ya tuntube mu a matsayin mu na dattawa.

0

RUSA MA AIKATAR WATSA LABARAI…..Ba wanda ya tuntube mu a matsayin mu na dattawa.
@ katsina city news
Daga ra ayin da muka samu a rubutun waya.daya daga cikin dattawan katsina ya rubuto ra ayinshi.amma ya Nemi a sakaya sunan shi.ga sakon shi;
.Danjuma, naga rubutun da da jaridun ku keyi.amma ni na dauka har yanzu maganar tana bisa shawarar ce.
Wani lokaci a baya , ina katsina naje na yi gaisuwa ga mai martaba .amma maganar bata hada mu ba.
Malam mamman Daura , yace, yaji labarin, wai.shi ma baya da tabbaci kamar yadda ya fada mani.
Abin da nake son jawo hankalin ku.a dokar kasa gwamnatin jaha na da iko dari bisa dari akan kasar ta.don haka komai tayi, bata Saba ba a doka ba.
A kuma tsarin zaman takewa, in mai mulki yaga dama yakan tuntubi shawara.in ya nema ana iya bashi.
Masari dattijo ne,kuma yasan darajar shawara.a shekarunshi da darasin rayuwarshi da kwarewarsa a siyasa ina shakkun yayi abin nan, bai Nemi shawara ba.
Don haka,har yanzu ina shakku.
Za a samu bambancin ra ayi,tsakanin matasa da dattawa da masu ra ayin mazan jiya.
Amma misali na hankali shine, idan wurin yana hannun gwamnati zai iya kara wasu shekaru dari a gaba . al umma na amfana.gwamnati na iya shawara akan sarrafa shi.asali ma can, gwamnan soja sarki muktar yana da rai,ya taba yunkurin hade wajen da dakin karatu.amma aka bar maganar sai an samu kudi.
Ginin dakin karatun katsina,anyi shi tun katsina na karamar hukuma. Shine kadai ne,ginin da ba a haba ka.labarin yana da tsawo ka same ni ranar jumma a da yamma.
Wannan wuri in ya koma hannun Dan kasuwa bayan wasu shekarun ba asan Wajen wa zai koma ba.wata Rana zai fada hannun magada kila kowa na da ra ayinshi.wani inyamuri na iya sayen wajen magada.
Kuma kamar yadda ka fadi wurin nan ya Dade..ni yanzu ina da shekaru sama da Saba in ,kuma haka muka tarar da wurin .
In har an tambaye mu, shawara, zamu bada .in kuma gwamnati ta yanke shawarar ta,to Allah sawwaka.
Allah ya saka maku da Alheri akan sauke nauyin dake kanku.tarihi ba zai manta da hakan ba,kunyi nasara ko ba kuyi ba.
Na gode.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here