Wayyanan Yaran Da Kuke Gani Yan Gida Daya Ne Suna Daga Cikin Daliban Da Aka Sace A Makarantar FGC Birnin/Yauri

0

Wayyanan Yaran Da Kuke Gani Yan Gida Daya Ne Suna Daga Cikin Daliban Da Aka Sace A Makarantar FGC Birnin/Yauri Dake Jihar Kebbi Tsawon Kwana Dari Da Doriya.

Daga: Mubarak Bala Argungu.

Wata yar uwar daya daga cikin daliban na tattauna da ita ta kafar sada zumunta watau WhatsApp take gayamin irin halin da suke ciki game da cigaba da rike yayan su da akeyi cikin daji suduka gidansu daya sai dai ba mahaifiyar su daya ba, hasalima daya daga cikinsu mahaifiyarta ta rasu sanadiyar bakin cikin abinda ya faru da yar’ta domin kuwa an riga ansaka lokacin auren yar tata da zarar ta gama makaranta a karshen wannan shekara saboda tana ajin karshe ne watau (SS3) sai kuma wannan al’amari yazo ya faru wannan yayi sanadiyar ta kwanta asibiti tsawon sati uku Sai Allah yamata cikawa.

See also  Ƙauraye a Katsina sun Jikkata Mutane a Unguwannin Rahamawa, Abatuwa da Janbango

Yanzu sun fara yanke tsammani gameda lamarin yayan nasu domin kuwa su a ganinsu matakan da hukumomi ke dauka basu taka kara sun karya ba wajen ganin an kubutar da yayan nasu.

Mafi yawan iyaye sun cire yayan su daga makaranta sanadiyar fargabar wannan abinda ya faru. Kullum suna kwana suna tashi da bakin cikin halinda yayan nasu suke ciki. Abin akwai ban tausayi matuka.

Muna rokon alfarmar yan uwa ma abota wannan kafa ta sada zumunta musamman wayanda keda kusanci da mahukunta dasu cigaba da yin tuni ga hukumomi akan lamarin yaran nasu. Allah da ya juyo da hankalin mahukunta akan wannnan lamari ya kuma kubutar da wayannan yaran acikin aminci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here