Direban dake kai fasinja wajen ‘yan bindiga don a yi garkuwa da su ya shiga hannu

0

Direban dake kai fasinja wajen ‘yan bindiga don a yi garkuwa da su ya shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta yi holan Hamisu Sule wani direba dake daukar fasinja yana tsayawa da su a daidai wajen da ‘yan bindiga suke fitowa domin suyi garkuwa da mutane.

A cewar kakakin rundunar’yan sandan babban birnin tarayya Abuja Frank Mba, shi wannan direba, bakinsa daya da ‘yan bindigar dake sace mutane suna yin garkuwa da su, idan ya dauko mutane sai yazo wajen da ya san ‘yan bindigar na labe sai ya nuna mota ta samu matsala.

Daga bisani kuma sai ‘yan bindiga su fito daga daji su yi awon gaba da mutane. Mba ya kara da cewar, sun samu bayanan sirri akan direban dan haka suka dana masa tarko har suka kamo shi.

See also  BRAND NEW 100-BED MOTHER AND CHILD HOSPITAL AT OKRIKA TOWN, RIVERS STATE!

Haka nan kuma Kakakin rundunar ya bukaci mutane da su daina hawa mota a bakin hanya ba tare da sun shiga tasha ba.
Mun dauko daga shafin daily Nigeria hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here