Zaban Shugaban Jam’iyyar APC: Abinda Aka Tattauna Tsakanin Dahiru Mangal Da Bala Abu Musawa

0

Zaban Shugaban Jam’iyyar APC: Abinda Aka Tattauna Tsakanin Dahiru Mangal Da Bala Abu Musawa

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

A cigaba da yakin neman shugabanci jam’iyya a matakin jihar Katsina wanda yanzu ta bayyana cewa mutane biyu ne suka nuna sha’awarsu ta neman wannan babar kujera.

Wato dai Bala Abu Musawa wanda shi ne mataimakin jam’iyyar na yankin Funtua sai kuma Malam Shitu S. Shitu wanda shi ke rika da jam’iyyar shekaru hudu da suka gabata, yana kara daukar sabon salo a matakai daban-daban

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewa hamshakin dan kusawa kuma jigo a siyasar Katsina, Alhaji Dahiru Barau Mangal ya yi ganawar sirri a jiya Litinin da Bala Abu da tawagarsa a gidansa da ke Katsina

Wannan ganawa dai na a matsayin wata manuniya da ke nuna inda hamshin ya karkata kansa wajan ganin Bala Abu ya samu shugabancin jam’iyyar, a matakin jiha wanda ake ganin yana da jama’a masu goyan bayansa.

Majiyarmu ta ce, Dahiru Mangal ya yi zaman sirri ne tare da wasu ‘yan majalisu guda 27 na jihar Katsina da kuma jiga jigan yakin neman zaban Bala Abu Musawa domin jin yadda tsare tsaran tafiyar yake.

“Bala Abu na gamsu da yadda kake tafiyar da al’amuranka babu hayaniya babu rigima ko tada hankali, kuma duk abinda kake cikinsa ko menene ni Dahiru Mangal kasa nunana a gaba, ina cikinsa tsundum” inji majiyarmu ta ce Dahiru ya fada da bakinsa.

Kazalika mai ba mu labarin ya ce, Dahiru ya yi mamakin ganin tarin ‘yan majalisar da suke biye da Bala Abu a wannan tafiya ta neman kujerar shugabancin jam’iyyar APC a matakin jihar Katsina.

Sai dai kuma a bangaran Bala Abu ya ki cewa komi game da wannan ziyara illa dai yana yawan cewa, yana yin wannan tafiya ne saboda jama’arsa da suka ce lallai ya fito neman wannan kujera tunda ya yi mataimaki har sau biyu sun gani kuma sun gamsu.

“Wallahi mun yi mamaki yadda Dahiru Mangal da kansa yasa ya kira Bala Abu kuma ya ce Bala din ya zo da duk wanda yake cikin wannan tafiya ta shi, kuma ya yi mamakin irin mutanen da ya gani acikin tafiyar Bala Abu Musawa” inji mai bada labarin.

Wannan ziyara ko ganawar sirri da ta gudana a tsakanin jigo kuma uba a siyasar jihar Katsina na nuni da cewa Dahiru Mangal na goyan bayan tafiyar Bala Abu duk da cewa a baya an yi zargin cewa tsohon Sanata Abu Ibrahim ne ya turo shi, zargin da Bala Abun ke cewa jama’arsa ne suke son ya yi takara.

Duk kokarin da muka yin na jin ta bakin Bala Abu Musawa domin jin ta bakinsa game da wannan ziyara abin ya ci tura, saboda an tsinke layin waya a garin Musawa inda yake zaune, saboda haka duk lokacin da muka ji daga bakinsa mun shaidawa duniya ke me wannan ziyara ke nufi?

El zaharadeen Umar shine wakilin sashen hausa na rediyon muryar musulunci dake kasar iran .
Yana kuma rubuta ma jaridun leadership hausa sharhi da labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here