A WURI NA QUNGIYAR POLO DAYA CE – Sarkin Katsina

0

A WURI NA QUNGIYAR POLO DAYA CE – Sarkin Katsina
A ranar asubucin nan ce ake sa ran kammala gasar wasan qwallon dawaki wato Polo wanda wannan wasa ke alamta buxe kakar wasan wannan shekara. Kazalika, kamar yadda aka sani kuma yake a al’adar wannan wasa, tun daga shekarar da Marigayi Mai Martaba sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya kawo wasan daga ƙasar Ingila a shekara ta 1920 ya zamo kuma kujerar shugabancin qungiyar na qasa yake a masarautar ta Katsina, wato, duk wanda yake sarki shi ne kuma shugaban qungiyar ta Polo kuma na din-din-din. Kazalika, yana daga cikin al’ada kaiwa Mai Martabar sarki ziyarar ban girma da ‘yan wasan kan yi gab da ana shirye-shiryen kammala wasan da kwana biyu ko daya.
Irin wannan ziyarar ce ‘yan wasan suka kaiwa Mai Martaba sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir a safiyar juma’ar nan domin nuna goyon baya tare da nuna cewa,’yan wasan suna nan tare da wannan al’ada wadda kuma zamo xaya daga cikin ziyarar da ake gani da muhammanci. Sai dai ba kamar yadda aka saba a baya ba, na aje ayi gaisuwa ayi raha tare da samun shawarwari daga sarkin, ziyarar ta wannan rana ta baiwa sarkin damar warware wata matsala ko tunani da wasu ke yi na cewa sarkin tamkar bai damu da sha’anin wasan ba wanda kuma za’a ce na xaya daga cikin abin da ya gada. Sarkin ya shaidawa ‘yan wasan dalilansa na zura masu ido bisa ga rarrabuwar da suka yi, bayan shi kuma a iya sanin shi, wasan Polo ko qungiyar Polo xaya ce. “Maganar NPA ko NPF ni a wuri na akan harkar Polo bata ma ta so ba, domin dukkan mu tsintsiya ce mai maxauri guda. Wannam warewar ita ta janyowa wasan cikas tare kuma da raba kawuwanmu bayan a can baya muna faxuwa da tashi tare, amma saboda wannan yau, sai a wari gari idan ‘yan wasan Kano ko Katsina ko Zariya ko ma wani wurin zasu yi wasa sai a taras waxancan ba su je ba kawai wai saboda ni ina NPA ko NPF. To ina jan hankalin ku tare da sanar da ku cewa, ni a wuri na, qungiyar Polo guda ce, sai dai ace mani tima-timai wanda kuma dama can da sunan haka ake buga wasan ba NPF ko NPA ba. Don haka, ku je ku sake haxe kan ku kamar yadda aka san mu tun can baya”, kamar yadda Mai Martaba sarkin ya ce a wajen wannan ziyarar ban girma da aka kaiwa sarkin Dokta Abdulmumini Kabir wanda kuma shi ne shugaban qungiyar na qasa.
Tun farko sai da shugaban kungiyar na Katsina wanda kuma shi ne Danmadamin Katsina Alhaji Usman Usman ya shaidawa sarkin irin yadda aka gudanar da wasan acikin kwanciyar hankali, da kuma bin doka da oda tare kuma da nuna godiya ga masarautar akan irin yadda take bayar da gudunmuwar na ganin ana aiwatar da wasan kamar yadda aka saba.
Kakakin kungiyar Polon na Katsina Kabir Ahmed S/kuka ya shaidawa manema labarai haka bayan kammala wannan ziyara a ranar wannan juma’ar a fadar Maimartaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here