INA ZA MU SA KAN MU!
…’Yan Kasuwar Gaban Green House
Muazu hassan
@Katsina City News
Sama da mutane 500 ke kasuwanci a gaban tsohuwar Ma’aikatan Hukumar Watsa Labarai da ke kallon ginin Green House, Katsina.
‘Yan kasuwar sun dauki sama da shekaru 25 suna sana’o’in siyar da yadi da takalma a wajen.
Sana’arsu ta kawo wa wajen albarka, har wasu suka zo suka gina manyan shaguna. Duk da haka rabonsu daga Allah bai taba kaucewa ba, suna da kwastomominsu.
‘Yan kasuwar sun fada wa jaridun Katsina City News cewa, da suka ji rade-radin za a siyar wa wani dan kasuwa ginin, sun yi gungu suka je wajen Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa, inda suka kai masa koke da korafi a rubuce.
Suka ce da farko ya nuna masu bai da masaniya, amma zai bincika da suka kara komawa suka roki a taimaka masu da wani filin inda za su koma, sai ya bude baki ya yi masu magana sosai.
‘Yan kasuwar sun ce a wajen mutane 350 ke da wuraren kasuwanci, sannan suna da yara sama da 100 masu taimaka masu.
Sannan sun ce dukkaninsu magidanta ne, masu iyali. Sun fada mana sama da baki 2.000 ya dogara da wannan wurin sana’ar tasu.
Suka ce wanda aka ba shi wajen da yake son tada su, gwamnati ta ba shi katafaren fili bai gina ba. “Yana cikin wadanda aka ba Katsina Mall, amma mu bayin Allah masu karamin karfi ana son a kammala murkushe mu”, in ji daya daga cikin ‘yan kasuwar.
Mun ji ‘yan kasuwar suna ta tattauna matakan da za su dauka na wannan fin karfi da kin sauraren su da suke zargin ana son a yi masu.
Wasunsu har sun fara Sallah da Alqunuti a filin da nufin kai kokensu ga Allah.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245