Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18.

0

Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Ana sauran wata daya daidai da zaben gwamnan jihar Anambra, hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta (INEC) ta saki sunayen yan takaran zaben na karshe.

Legit ta tattaro cewa a wannan jerin sunaye na karshe, hukumar ta sanya sunan Valentine Chineto Ozigbo matsayin dan takaran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Zaku tuna cewa a jerin sunayen da INEC ta saki a baya, jam’iyar PDP bata da dan takara saboda rikice-rikicen kotu.

Festus Okoye, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan jama’a a jawabin da ya saki a shafin Facebook cewa jam’iyyun siyasa 18 zasu yi takara a zaben 6 ga Nuwamba.

Ga jerin yan takaran da INEC ta saki:

1:- Ekene Alex Nwankwo (Jam’iyyar Accord A).
2:- Doreen Ifeoma Madukaarisa (Jam’iyyar Action Alliance, AA).
3:- Obi Sylvester Chukwudozie (Jam’iyyar African Action Congress, AAC).
4:- Akachukwu Sullivan Nwankpo (Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC).
5:- Prince Ume-Ezeoke Afam Luke Douglas (Jam’iyyar Action Democratic Party, ADP).
6:- Emmanuel Andy Nnamdi Uba (Jam’iyyar All Progressives Congress, APC).
7:- Chukwuma Michael Umeoji (Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA).
8:- Eze Robinson Chukwuma (Jam’iyyar Allied Peoples Movement, APM).
9:- Azubuike Philip Echetebu (Jam’iyyar Action Peoples Party, APP).
10:- Chika Jerry Okeke (Jam’iyyar Boot Party, BP).
11:- Agbasimalo Obiora Emmanuel (Jam’iyyar Labour Party, LP).
12:- Ohajimkpo Leonard Emeka (Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP).
13:- Adaobi Uchenna Okpeke (Jam’iyyar National Rescue Movement, NRM).
14:- Valentine Chineto Ozigbo (Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP)
15:- Nnamdi Nwawuo (Jam’iyyar Peoples Redemption Party, PRP)
16:- Ekelem Edward Arinze (Jam’iyyar Social Democratic Party, SDP).
17:- Ifeanyi Patrick Ubah (Jam’iyyar Young Progressive Party, YPP)
18:- Ugwoji Martin Uchenna (Jam’iyyar Zenith Labour Party, ZLP).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here