Yadda fara take rufawa mutane asiri a jihar Borno.
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Dubban mutane suka dogara da sana’ar kama fara da sayar da ita a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mafi yawan masu wannan sana’a dai mata ne da suke saya daga mutanen da suka kamata a cikin daji, sannan su soya su kuma su sayar da ita ga jama’ar jihar.
Mutan Borno sun dauki fara a matsayin wani abincin marmari da mata da maza da yara da manya suke ci.