BALA ABU MUSAWA MUKE SO!

0

BALA ABU MUSAWA MUKE SO!

In ji mahalarta taron Daura 2023

Abubakar Abdullahi
@Katsina City News

A ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu jigajigai a yankin Daura karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Borno, Kanal Abdulmumin Aminu suka gudanar a dakin taro na Daura Motel, ya samu halartar manyan ‘yan siyasa da masu rike da mukamai na siyasa daga yankin Daura.

Manufar taron, kamar yadda wadanda suka shirya shi suka bayyana, ya hada da jawo hankalin jama’ar Jihar Katsina a kan cewa ya kamata a shekarar 2023 dan takarar Gwamnan Katsina a jam’iyyar APC ya fito daga yankin Daura.

Bayan kammala taron, Wakilan jaridun Taskar Labarai da suka je wajen sun rika bi mahalarta taron daya bayan daya suna tambayarsu, wa suke ganin ya kamata ya zama Shugaban jam’iyyar APC a zaben da za a yi ranar Asabar mai zuwa?

Tambayar daya suka rika yi masu ita ce tsakanin Malam Shittu S. Shittu da Bala Abu Musawa wa ya kamata?

Duk wadanda muka tunkara amsa daya suke badawa, Bala Abu Musawa.

An tambaye su me ya sa suke cewa wa ke maganar Malam? Sai suka ce ai tsarin jam’iyyar APC ta kasa ya janye shi.
Kuma Bala Abu Musawa da shi aka faro tafiyar nan, kuma dan siyasa ne, matashi manomi da ya taso cikin talakawa daga karkara.

See also  KOTU TA DAKATAR DA JAM'IYYAR PDP TA JIHAR KATSINA DAGA YIN ZABEN SHUGABANNIN JIHA

Sun ce Bala Abu Musawa ba zai yi siyasar boko ba, zai yi siyasa ce ta ‘yan siyasa da sanin darajar siyasa.

Wata mata a taron ita kadai ce ta dage sai Malam Shittu har ma ta so ta mayar da jin ra’ayin kamar fada.

Ga yadda hirar ta su ta kasance; “Kai ka ce daga ina kake?” Ya ba ta amsa Katsina City News.

Sai ta ce; “Wadannan masu bata mutane?” Sai Wakilinmu ya ce; “Wa muka bata?

Ta yi shiru ta ce; “Ai na san ku, har wannan Shugaban naku baki Dan Kicicciri”.

Wakilinmu ya dage a kan Hajiya ta bayyana wa muka bata? Ba amsa.

Da ya juya zai tafi sai ta ce; “Sai Malam Shittu!” Tana da dariyar kata.
Amma duk wadanda aka yi magana da su fadi suke Bala Abu Musawa ne zabin su.

Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here