Buhari ya gaza cika alkawarin da ya dauka a bangaren ilimi a kasafin 2022

0

Buhari ya gaza cika alkawarin da ya dauka a bangaren ilimi a kasafin 2022.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gaza cika alkawarin da ya dauka na kara yawan kudaden da zai kashe a fanin ilimi da kashi 50 cikin 100 nan da shekaru biyu masu zuwa, kamar yada bayanan kasafin kudin 2022 da ya gabatarwa majalisa ke tabbatarwa.

Buhari ya alkawarta hakan ne a lokacin taron ilimi na duniya da aka gudanar a Landan.

A lokacin taron shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran kasashen duniya wajen sanar da alkauran inganta fanin ilimi da karin kudaden da ake warewa.

Masu sharhi kan kasafin 2022 na cewa shugaba Buhari ya warewa fanin ilimi N875,925,404,037 (ciki harda kudaden da aka warewa UBEC N139,236,349,701) cikin kasafin N16.9tn da ya gabatawa majalisa.

Wannan na nufin ɓangaren ilimi an ware masa kashi 5.3 cikin 100 wanda ke nuna an sake samun koma-baya idan aka kwatanta da kashi 5.6 cikin 100 na kasafin 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here