Gwamnan jihar Zamfara Ballo Matawalle ya ƙalubalanci shugabannin siyasa a jiharsa su fito su rantse cewa ba su da hannu da matsalar tsaron jihar.

0

Gwamnan jihar Zamfara Ballo Matawalle ya ƙalubalanci shugabannin siyasa a jiharsa su fito su rantse cewa ba su da hannu da matsalar tsaron jihar.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Gwamnan jihar Zamfara Ballo Matawalle ya ƙalubalanci shugabannin siyasa a jiharsa su fito su rantse cewa ba su da hannu da matsalar tsaron jihar.

Gwamnan wanda ya sa kwamishinoninsa shan rantsuwa da Allah da Al’Kur’ani ya ce ya yi ne saboda ƴan adawa da ke zargin cewa akwai jami’an gwamnati da ke da hannu da matsalar tsaron da jihar ke fama da ita.

Ya ce ya rantse kuma ya sa ma’aikatan gwamnatinsa yin rantsuwa, don haka kuma yake ƙalubalantar ƴan adawa su fito su rantse.

“Idan kasan ba ka da hannu da hakarar ta’addanci to ka fito ka rantse ka wanke kanka ga al’umma,” in ji Matawalle.

See also  YADDA 'YAN BINDIGA SUKE CIN KARENSU BA BABBAKA A BATSARI

Rantsuwar da kwamishinonin Matawallae suka yi rungume da Al-Kur’ani ta ƙunshi cewa:

“Billahillazi La’ilaha illahuwa, na rantse da Allah cewa ban taɓa shiga sha’anin ta’addanci ba, a jihar Zamfara ko kuma na yi amfani da wata dama da Allah ya ba ni domin in nuna jin dajin ana kashe al’umma ko salwantar da dukiyarsu. Haka kuma ban taɓa jin daɗin aikin ta’addanci da ke gudana a cikin jihar nan ko kuma a wajenta ba.

“Idan ina da hannu a cikin ta’addancin kar Allah ya ba ni lamuni ko da na dakika ɗaya. Haka kuma ba zan yi amfani da mukamina ba domin taimakawa wajen aikin ta’addanci ko salwantar da dukiyar jama’a. Idan na yi haka kar Allah ya ba ni abin da nake nema duniya da lahira.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here