Sheikh Abduljabbar Kabara ya ƙalubalanci lauyoyin da ke kare shi a kotu

0

Sheikh Abduljabbar Kabara ya ƙalubalanci lauyoyin da ke kare shi a kotu

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Fitaccen malamin addini musuluncin nan a Kano Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda sabbin lauyoyinsa ke kare shi a kotu kan bayyana shaidu da suka gabatarwa kotu.

Abduljabbar ya bayyana hakan ne a yayin zaman kotun na yau Alhamis da ya gudana a babbar kotun musulunci da ke kofar Kudu a birnin Kano.

A yayin zaman kotun karkshin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, alkalin ya fara ne da tambayar sabbin alkalan Abduljabbar tuhume-tuhume da suka bukaci daukaka ƙara.

Umar Mohammd da ke jagorantar tawagar sabbin lauyoyin, ya ce sun sauka daga kan bukatar daukaka kara, amma suna nan kan bakar su na rashin hallacin tsayawar lauyoyin da gwamnati ta dauka masu mukamin SAN da kuma batun gabatar da sabon caji.

See also  MAHARA SUN KAI HARI BATSARI

Sai dai farfesa Mohammad Lawan Yusufari lauyan da ke gabatar da kara ya ce kotu na iya bayar da hukunci kan batun hallacin tsayawarsu a gaban ta.

Bayan amincewa da hakan yasa mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bukaci masu kara da su gabatar da shaidun da aka bukace su.

A yanzu dai kotu ta sake dage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Oktoban da mu ke ciki domin sake wani zaman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here