A yau ne ake sa ran za a ci gaba da shari’ar jagoran ‘yan awaren Najeriya Nnamdi Kanu a Abuja.
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Ana tuhumar Mista Kanu – jagoran kungiyar IPOB da laifin ta’addanci da cin amanar kasa, da kuma gudanar da wani kamfanin buga labaran batanci da ke yi wa jama’a ingiza mai kantu ruwa.
An samu hatsaniya a watan Yuli lokacin da hukumomi suka kasa gabatar da shi a gaban kotu don yi masa shari’a. An fara kama shi ne a shekarar 2015, amma ya tsere daga Najeriya bayan ba da shi beli a shekarar 2017, kafin daga bisani aka sake kamo shi a watan Yunin wannan shekarar.
Yana iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai idan aka same shi da laifi.