Trump zai bude shafin Intanet mai kama da Facebook da ya radawa suna Gaskiya da Gaskiya
Rahoto: Comrade Musa Garba Augie.
Donald Trump ya sanar da shirin kaddamar da wani sabon shafin sada zumunta.
Shafin wanda zai sanya wa suna Gaskiya da Gaskiya, zai kasance karkashin gudanarwar wata kungiyar da ke kula da harkokin kimiyya da fasaha a tafiyarsa ta siyasa.
Tsohon shugaban ya ce zai kirkikiri kamfanin ne da fatan jama’a za su yi abun da ya kira zaluncin manyan kamfanonin fasaha, irinsu Facebook da Twitter bara’a.
Ana sa ran Shafin Gaskiya da Gaskiya na Mista Trump, zai fara aiki a watan Nuwamba tare da wasu kayyadaddun mutane da za su fara amfani da shi a matsayin gwaji, kafin daga baya ya zama na kowa da kowa.
A baya dai shafukan Facebook da na Twitter suka rufe shafin tsohon shugaban Amurkan saboda harin da magoya bayansa suka kai wa majalisar kasar.