Wataƙila nan da shekara uku ku fara hawa tasi mai tashi sama

0

Wataƙila nan da shekara uku ku fara hawa tasi mai tashi sama

Daga Bernd Debusmann Jr

Business reporter

Wani rahoto ya yi hasashen cewa daga nan zuwa shakerar 2040 za a samar da irin wannan mota guda 430,000 a faɗin duniya.

Da zarar aka yi batun tasi mai tashi sama don kai mutane anguwa a cikin gari, abin da ke fara zuwa zukatan wasu shi ne sanannen fim dinnan na zane wato ‘The Jetsons’.

Cartoon din wanda aka yi a shekarar 1960 ya nuna wasu iyalai da ke rayuwa a wani gari na zamani, inda mutane ke zuwa aiki cikin wasu motoci da ke tashi sama.

Shekaru 20 a karni na 21, wasu masana kimiyya na kokarin mayar da mafarkin waɗanda suka shirya cartoon din Jetsons gaske.

A yanzu kamfanonin Uber da Boeing sun samar da motoci masu tashi sama.

Wani rahoto ma ya yi hasashen cewa daga nan zuwa shekarar 2040 za a samar da irin wadannan motoci guda 430,000 a faɗin duniya.

Wannan kuma na zuwa a dai dai lokacin da ake ci gaba da samar da jirage marasa matuki, da ake hasashen kasuwar su za ta bunkasa da fam biliyan hudu daga nan zuwa 2028.

To amma kafin a samu yadda ake so wurin wadatuwar waɗannan motoci da kuma jirage marasa matuki akwai bukatar birane su gina kananan tashoshin jirgi da masana suka saka wa suna “skysports”.

Dole za a bukaci samar da waɗannan tashoshi don motocin hayar su samu wurin sauka don daukar mutane.

Kamfanin Joby Aviation na California a Amurka na gaba-gaba wurin samar da tasi mai tashi sama, don tuni ya gudanar da gwajin fiye da guda 1,000.

Kamfanin na fatan samun amincewar hukumar sufurin jiragen sama ta Amurka don fara aiki a shekarar 2024.

Motocin Joby za su iya daukar fasinjoji hudu, kuma za su iya tafiyar kilomita 322 a cikin awa ɗaya.

“Abin da muke so mu yi shi ne samar da wadatattun motoci a wuraren da ake bukatarsu,” a cewar Oliver Walker, mai magana da yawun kamfanonin Joby.

“Muna aiki da hukumomi a birane don tabbatar da cewa an samar da tashoshin da waɗannan motoci za su rika yada zango.”

“Abin da muke so mu yi shi ne samar da wadatattun motoci a wuraren da ake bukatarsu,” a cewar Oliver Walker.

Joby ya hada hannu da kamfanin fasaha na Reef Technology, da nufin amfani da rufin garejin motocinsa.

See also  Najeriya Kasarmu Ta Gado.

Duk da shirin samar da motoci masu tashi sama ba magana ce ta yanzu-yanzu ba, batun na samun karɓuwa daga hukumomi a Amurka.

Tuni garuruwan Houston da Los Angeles da kuma Orlando suka fara shirin samar da tashoshin motoci masu tashi sama.

A cewar magajin garin Los Angeles Eric Garcetti, samar da motoci masu tashi a birane ba karamar nasara ba ce.

Amurkawa da dama na gani tsarin zai rage cunkoson ababen hawa a tituna kasar

A Birtaniya gwamnati ta yi maraba da shirin samar da tashar motoci masu tashi sama a kusa da wani filin kwallo da ke Coventry.

Sai dai masana sun bayyana cewa akwai kalubale da dama da suka yi tsayuwar gwamin jaki ga samar da tashohin motocin.

“Kafin a samu nasarar ganin waɗannan motoci sun yi aiki yadda aka gani a shirin Jetsons sai an shawo kan wasu matsalolin tun yanzu”, a cewar Jennifer Ritchter, kwararriya kan jirage marasa matuki da kuma tasi mai tashi sama.

Wani gwaji kan yadda karamar tashar jirgi za ta kasance a birnin Coventry na Birtaniya

Aaaron Belbasis, masani kan harkokin fasahar zamani ya ce batun lafiya da kariya na da matukar muhimmanci a wannan batu.”

Ya kara da cewa “idan har aka ce za a samu yawaitar motoci a sararin samaniya to akwai yiwuwar haɗari, ko kuma idan aka yi rashin sa’a mota ta fado babu shiri.”

“Haka kuma idan mota ta fado ba wai wadanda ke ciki kawai za ta jikkata ba, har da wadanda za ta fado a kansu,” a cewar Mr Belbasis.

An jima da yin gwajin jirgi marar matuki da ke isar da sako

Wasu masanan na ganin cewa akwai bukatar zuba jari wurin samar da tashoshi isassu ba wai a mayar da hankali wurin samar da motoci babu isassun filayen tashi da saukar su ba.

A cewar Ricky Sadhu duk da kalubalen da ke da akwai, akwai kuma haske ta ɓangaren bukata da sha’awar samar da tashoshin motoci masu tashi a biranen Amurka da Turai da kuma Asiya.

”Muna da burin ganin an samu tashoshi 200 a faɗin duniya cikin shekaru biyar,” a cewar Sadhu, kuma duk da haka manyan birane za su bukaci fiye ma da haka.”
BBC HAUSA ✍

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here