Wata ƴar ƙungiyar agaji ta Matasa Musulmai ƴan Najeriya (YMCN) da aka fi sani da Munazzamatul Fityanul Islam ta rasa ranta yayin tattakin murnar ranar Mauludi a Abuja

0

Wata ƴar ƙungiyar agaji ta Matasa Musulmai ƴan Najeriya (YMCN) da aka fi sani da Munazzamatul Fityanul Islam ta rasa ranta yayin tattakin murnar ranar Mauludi a Abuja, babban birnin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, sannan wasu mutum 10 sun suma.

Dubban Musulmai ne da suka haɗa da ƴan Islamiyya da mambobin ƙungiyoyin agaji da sauransu suka taru daga sassan Abuja suka yi maci a kan tituna don murnar ranar.

Ministan Abuja Muhammadu Musa Bello ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari a wajen taron.

A lokacin da take magana kan faruwar lamarin, wata jami’ar ƙungiyar agaji malama Sajida Bala Abdullahi ta ce marigayiyar mai suna Asma’u mai shekara 20 ta je taron ne daga unguwar Kuje.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here