Zulum ya lashi takobin kawo ƙarshen bangar siyasa a Borno
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi gargaɗin cewa duk wani ɗan siyasa da aka kama da ɗaukar nauyin ƴan bangar siyasa a jihar zai fuskanci hukunci yadda ya dace da shi, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta ɗauki rashin ɗa’a ba.
Gwamnan ya yi gargaɗin ne ranar Litinin a gidan gwamnati a lokacin da yake jawabi a gaban shugabannin wata ƙungiya ta ƴan bangar siyasa.
Wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan kafofin yada labarai, Isa Gusau, ya fitar ta ce gwamna Zulum ya sha bayar da umarnin ayyuka da shirye-shiryen koya wa al’umma hanyoyin dogaro da kai ga ƙungiyoyin don mayar da su halatattu.
Jihar ta ce duk da waɗannan matakan, gwamnan ya koka kan yadda mafi yawan matasa a jihar suka ɗauki bangar siyasa a matsayin sana’a.