BOKO HARAM TA KUSA ZUWA TARIHI

0

BOKO HARAM TA KUSA ZUWA TARIHI …Inji BULAMA BUKARTI
Muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Daya daga cikin masana akan yan kungiyar boko haram Barista Bulama Bukarti ya rubuta cewa ga dukkan alamu boko haram ta kusa zuwa karshe.
Bulama Bukarti Wanda sannnen mai bincike ne akan boko haram kuma Wanda ke tare da cibiyar binciken toni bileya dake da mazauni a kasar ingila birnin London.
Bukarti, Wanda hatta mataccen shugaban boko haram shekau, ya taba yanke masa hukuncin kisa akan magana da rubutu da ya keyi akan boko.
Bukarti yayi wani rubutu a shafin sa dake fitowa duk sati a jaridun daily trust ta ranar laraba 20 ga watan oktoba 2021.
Rubutun mai taken “”wannan kamar shine mafarin karshen boko haram da fatan ..zai a kara kaimi””
A rubutun yace mutuwar shekau ta kawo rauni sosai a boko haram bangaren shekau.
Hakan ya sa, dubban yan bangaren shekau suka gwammace su mika kansu ga gwamnatin Najeriya. Ko su ajiye makamansu.wasu kuma suka sha alwashin daukar fansa.
A rubutun na Bukarti ya ce,mutuwar shekau ta haifar da wani fadan cikin gida tsakanin boko haram da iswap.
Kwatsam sai shima shugaban iswap al barnawi ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wani fada da bangaren shekau masu neman fansa.
Bukarti yace yanzu mutuwar al barnawi sai ta kara raunana iswap.fadan cikin gida sai ya kara fadada tsakanin iswap da bangaren shekau.
Bukarti yace, yanzu dukkanin bangarorin biyu iswap da boko haram, basu da wani jagora mai kwarjini.da zai iya jagorancin su.don haka boko haram da iswap zasu koma sai dai su rika kokarin ya zasu cigaba da rayuwa?
Bukarti yace sauran kwamandojin da suka rage zasu iya rika kai hare haren karfin hali.amma ba za zasu iya Dorewa ba.
Bukarti yayi Kira ga gwamnati da jami an tsaron mu,suyi amfani da wannan nasarar da ta samu daga Allah.don kammala murkushe boko haram.
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here