DAN MAJALISAR TARAYYA YA BUDE WAJEN CIN NAMA DA SHAN SHAYI A KATSINA

0

DAN MAJALISAR TARAYYA YA BUDE WAJEN CIN NAMA DA SHAN SHAYI A KATSINA.
@ katsina city news
Alhaji mansir Ali mashi Dan majalisar tarayya mai wakiltar mashi da dutsi a jahar katsina
Ya bude zahra da Iman kitchen domin sayar da gasashshen Rago,tsiren kaji,da na hanta,Kundu da kuma Nama da shan shayi da abinci.
A jiya asabar 23/10/2021 aka yi bukin bude wajen da bayar da komai kyauta ga wadanda suka je don bukin budewa.
A zahra da Iman kitchen, za a rika sayar da naman Rago datse,da tsiren kaji da kuma nama da hanta da Kundu.
Akwai kuma sashen cin abinci.da shan shayi.dan wajen hutawa don tattaunawa.
Yan uwa da abokan arziki suka cika wajen domin taya Dan majalisar tarayyar murnar bude wannan wajen arzikin.
Wanda irin sa ne na Zamani a jahar ga kuma samar da aiki da akayi a wajen .
Zahra da Iman kitchen na bisa titin lawal kaita daf da kwanar shiga liyafa palace.daura da safalma motors.


Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here