Buhari zai tafi Saudiyya Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi Saudiyya ranar Litinin domin halartar wani taron zuba jari a Riyadh.
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Fadar shugaban cikin wata sanarwa ta ce Buhari zai halarci babban taron na kwana uku wanda zai ƙunshi manyan ƴan kasuwa daga Najeriya da manyan masa’antu da masana makamashi domin tattauna batutuwa da suka shafi makomar saka jari a duniya.
Bayan kammala taron shugaban na Najeriya zai gudanar da aikin Umrah kafin ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a, a cewar sanarwar.
Shugaban zai tafi tare da rakiyar jami’an gwamnatinsa da suka haɗa da ministan sadarwa Dr. Isa Ibrahim Pantami da ƙaramin ministan harakokin waje Ambasada Zubairu Dada da ministan man fetur Timipre Sylva da kuma mai ba shugaban shawara kan harakokin tsaro Janar Babagana Monguno.
Sauran ƴan kasuwa daga Najeriya da za su halarci taron sun haɗa da Alhaji Mohammed Indimi da Alhaji Aliko Dangote daTope Shonubi da Wale Tinubu da Alhaji Abdulsamad Rabiu da Hassan Usman da Omoboyode Olusanya da Abubakar Suleiman da Herbert Wigwe da kuma Leo Stan Ekeh.