Ƙungiyar Daliban Arewacin Najeriya ta karrama shugaban masu buƙata na ƙasa Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa da Lambar yabo ta girmamawa.

0

Ƙungiyar Daliban Arewacin Najeriya “National Association Of Northern Nigeria Student” ta karrama shugaban masu buƙata na ƙasa Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa (Sarkin Arawan Kabi), da Lambar yabo ta girmamawa.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Sun Ziyarci Sarkin Arawan Kabi, a fadar gidansa dake Gesse Phase! cikin garin Birnin Kebbi. Ƙungiyar ta karrama shi da lambar girmamawa kan gudummuwa da ƙoƙarin da yake yi, wajan ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya Addabi yankinmu na Arewacin Najeriya da ƙasa baki daya.

Ƙungiyar ɗaliban ta karrama Shugaban ne bisa ƙoƙarin da yakeyi na inganta rayuwar al’umma marayu da masu buƙata da al-ummar kasa baki daya, wajen bada gudummuwa ga Matasa don ganin sun tashi sun nemi Ilimi, da koyon sana’o’in Zamani.

Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa (Sarkin Arawan Kabi) Yayi kira ga dalibai dasu zama masu biyayya wajen neman ilimi saboda ilimi shine ginshikin na rayuwa, shine matakin na kowane bagire a rayuwa.

Daga karshe yayi addu’ar Allah ya zaunar da kasarmu lafiya da ci gaba mai amfani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here