MATSALAR TSARO A YANKIN BATSARI; INA AKA KWANA?
Daga Misbahu Ahmad Batsari
@Katsina City News
Tun bayan katse layukan sadarwa domin dakile hare-haren ‘yan bindiga, jama’a suka yi ta faman tunanin yadda za ta kasance, duba da yadda sadarwa take da matukar mahimmanci ga rayuwar al’umma. Sai dai hakan ya zama alheri ga mutanen yankin Batsari, domin an daina satar mutane domin karbar kudin fansa (kidnafin).
Wasu da muka zanta da su, sun bayyana mana cewa wannan nasara ba ta rasa nasaba da katse layukan sadarwa da aka yi. Saboda ta waya ake ciniki da sallama wadanda aka kama.
Amma kuma duk da saukin da ake ganin an samu bai hana ‘yan bindiga yin ta’asarsu a wasu wuraren ba, domin a cikin irin wannan yanayi suka je Yasore, inda suka kashe mutane 12, tare da kone masu gidaje, shaguna da rumbuna.
Sannan yanzu halin da ake ciki akwai wuraren da ba su shiguwa sai da rakiyar jami’an tsaro.
‘Yan bindiga na fuskantar karancin mai (fetur), saboda wani ya labarta mana cewa sun kama shi, suka kwashe man da ke cikin babur dinsa suka sake shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kuma sha kama mutane suce sai an kawo masu mai za su sake su. Hakan ta faru a kauyen Ruma tsohon gari da sauran su.
Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
O7043777779 08137777245