YADDA AKE CINIKIN DIGRIN GIRMAMAWA NA ‘DAKTA’ A WASU JAMI’O’I A KASASHEN WAJE.
…Binciken Musamman
Zainab Abdullahi
@Katsina City News
Binciken jaridun Katsina City News, ya tabbatar an kusa shekaru 20 ana cinikin digrin girmamawa na ‘Dakta’ a wasu Jami’o’in kasashen Afrika masu raunin tattalin arziki da wasu Jami’o’in kasashen Asiya da sukan bai wa wasu mutane daga Afrika.
Shekaru 17 da suka wuce wani Dan Majalisar Tarayya daga Katsina aka ba shi digrin girmamawa na dakta daga wata jami a a waje amma a wani dakin otal a Legas akayi bukin.
A wancan lokacin Dan Majalisar ya tabbatar wa da Wakilanmu cewa, Naira dubu 150 ya bayar. A zamanin mulkin gwamnatin Shema an bai wa Ciyamomin Kananan Hukumomi da yawa digrin girmamawa, wasu sun amsa, wasu sun ki yarda saboda farashin da aka ba su ya yi yawa.
Wasu takardun da jaridun nan take da su na digrin girmamawa da wasu makarantun Asiya kan bayar, ya nuna a shekarun baya suna amsar daga Naira milyan biyu zuwa sama.
Kuma kai za ka zabi inda za a ba ka. Ana iya aiko maka duk kwalaye da kambin digrin ” dakta” ta hanyar sako ka amsa, ka hada abokanka a rataya maka.
Ko ka dau nauyi wani ya zo ya kawo maka a shirya a ba ka, ko kuma ka je can. Kowane farashinsa daban.
A Katsina akwai Wakilan irin wadannan Jami’o’in masu ba da digrin na ‘dakta” don samun kudin ‘shiga daban.
A Katsina City News mun zanta da daya daga cikin su a ranar 28/10/2021, inda ya tabbatar mana yana wakiltar wata Jami’a a kasar Benin. Yana amsar dubu 500. Duk kuma wanda ya kawo mutane uku suka biya za a ba shi digrin ”dakta” daya kyauta.
Dubu 500 din kudin digrin na ”dakta” ne, amma akwai kudaden sauran shirye-shirye. Wannan kuma dai dai ruwa dai dai kurji.
A irin wannan taron bayar da wannan digri na dakta, ba a tara mutane da yawa, a dakin otal, ko wani ofis ake rataya shi. A dau hoto a dora a soshiyal midiya.
Wani kuma akan dan gayyato mutane, amma da ka bi hotunan za ka gane sojan haya ne.
A Jihar Katsina akwai irin takardun wadannan digrin na dakta girmamawar a teburorin manyan masu rike da mukaman gwamnati da yawa duk sun yi wancakali da su.
Wani Kwamishina ya ce: “Na ki amsa ne don na san buge ne da aka faro tun zamanin jam’iyyar PDP”.
Digrin girmamawan dakta na gaskiya sune wadanda manyan Jami’o’in kasar nan kan bayar, wanda sai an kafa kwamitin tantancewa, sai an yi bincike, sai masana sun wasa kwakwalwarsu, sannnan su amince bisa dalilai.
Kuma sukan bayar da su ne a taronsu na yaye dalibai, gaban shugabanni da kuma masana.
Wasu Jami’o’i masu ba da irin wannan digrin sai ka je ka iske ginin Firamare a Katsina ta fi ta girma, kuma su sun dauka kudin shiga suke samu ba wani laifi ko kuskure suke yi ba.
Wani rijistara na daya daga cikin Jami’o’in
ya tabbatar mana da haka. “Mu haja gare mu ta siyarwa. Za mu talata, mai so ya siya zai zo zai biya, mu siyar masa. Ina muka aikata laifi?”
Haka shima Wanda ya saka kudin shi ya amso ”dakta” babu inda yayi laifi.don kuwa kuturu da kudin shi.sai ya dulmuya ya tsunshi a kwaryar fura.
Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com