JUYIN MULKI A KAUYUKAN JAHAR SOKOTO

0

JUYIN MULKI A KAUYUKAN JAHAR SOKOTO

Ɗan bindiga Bello Turji da yaranshi sunyi juyin mulki a wasu kauyukkan Dake karamar hukumar sabon birnin jahar Sokoto.

Yanran Bello Turji da suka hada da Ɗan Bakkwalo, Boka l Tamiske, Hassan Ɗan Kwaro, DOGO da Jammu Baki sun gayyaci mazauna kauyukkan zaman tattaunawa a kauyen Saturu ranar alhamis 04/10/2021.

Yayin zaman ne suka umurci mazauna kauyen Gangara da su zabi daya daga cikin yan bindigar a matsayin hakiminsu Inda suka zabi dan bindiga Ɗan Bakkwalo a matsayin sabon hakinin gangara.

Nantake sabon hakimin gangara Ɗan Bakkwalo ya gindiya musu sharudda da suka hada da Bude kasuwanni da masallatai da sauransu.

See also  SOJA SUNYI MA YAN BINDIGA BARNA A NAHUTA BATSARI

A kauyen Maƙwaruwa Ɗan bidiga Boka Tamisƙe ya nada kanshin a matsayin hakiminsu Inda ya Kira Taron gaggawa da umurtar hakimin garin Mai suna Ɗan Sani da ya gayawa talakkawansa da Kansa cewa yanzu Boka Tamiske ne sabon hakiminsu ba Shiba.

Yanzu haka su ke da wuka da nama a waddannan kauyukkan.

© DailyStar Nigeria
Fassarar
Illela Daily Post

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here