CIN AMANAR KASA: SOJAN DA AKE ZARGI DA HANNU CIKIN HARIN NDA YA ZO HANNU

0

CIN AMANAR KASA: SOJAN DA AKE ZARGI DA HANNU CIKIN HARIN NDA YA ZO HANNU

 

Hassan Male

Wani soja Mai suna Torsabo Solomon yazo hannu a ranar litinin 8/11/2021 kan zargin da akeyi masa na kitsa harin yan’ bindiga da aka Kai a makarantar horas da sojoji ta NDA dake Kaduna.

Kamar yadda majiyoyin jaridar daily trust da DCL suka tabbatar, babban kwamandan base, 153 BSG dake Yola jahar Adamawa ne ya bayar da umarnin kama sojan biyo bayan bukatar hukumomin soji dake Kaduna su kayi.

Kamar yadda ganau su ka shaida an dauki sojan wanda yake a makarantar comprehensive na sojan sama dake Yola, zuwa Kaduna a cikin jirgi mai lamba NAF 930 da Karfe 8:15 na safe domin fuskantar tuhuma dangane da makamai da alburusai da aka yi amfani da su a harin na Kaduna.

Ya zuwa yanzu dai, babu wani jawabi da aka samu daga hukumomin soji dangane da wannan labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here