TSAKANINA DA GIDAN REDIYON VISION FM KADUNA

0

TSAKANINA DA GIDAN REDIYON VISION FM
KADUNA

-Malam Mahdi Shehu

Mu’azu Hassan
@ katsina city news

“A wani lokaci can baya, Umar Farouk Musa Shugaban gidan rediyon vision FM, Kaduna, ya same ni, ya yi mani koken NBC ta ba su lasin na kafa gidan rediyo a Kaduna, amma ba su da muhalli. Suna neman wuri haya.

“Ni na tuka shi a motata na kai shi gidan da ake rikici a kai. Na ce ya yi maku? Umar Faruk ya yi godiya. Na ce na bar maku ku zauna kyauta har zuwa bayan raina. Wannan magadana sai yadda suka yi da wurin.

“A nan Vision FM suka kafa gidan rediyonsu na Kaduna. Tun daga lokacin ba abin da ya sake shiga tsakaninmu.

” A matsayina na dan kasa, dan Jihar Katsina na rika magana a kan abin da ke faruwa a gwamnatin Katsina.
Vision FM sai suka zama dandalin cin mutuncina.
Na yi magana da Umar Faruk, ya ce zai sa baki. Da na ga abin ya ki tsayawa, na ce ina neman a ba ni dama in biya Naira milyan biyu a bude waya ga mutanen Katsina, in ba da amsa, Umar ya ki amincewa, kamar yadda Shugaban Vision FM na Katsina ya tabbatar mani.

“Na hakura. Duk a haka a gidana Vision FM Kaduna ke zama kyauta. Sai na ga ina bukatar gidana, sai na rubuta masu takarda cewa na ba su shekara daya su ba ni gidana.
Daga baya na je gidan na ga cewa ba su kafa dogon karfen watsa shirye-shirye ba. Sai na sake rubuta masu wata wasikar na ce na canza daga shekara daya, zuwa wata shida. Domin na lura ba su kafa karfen ‘mass’ ba.

“Sai Vision FM suka rubuto mani cewa su za su tashi ne kawai bayan shekara daya. Sai na ba su amsa, ban amince ba. Bayan wata shida ta cika na kyale su na kara masu har wasu watannin.

“Wata rana na je ginin na cire wasu kayan da ke gidan wadanda nawa ne, kamar get da wayar wutar lantarki da kuma tankin ruwa.

“Muna ciki ‘yan sanda suka zo suka tafi da mu. Muka je har gaban Kwamishinan ‘yan sanda na ba shi takardu na kora masa bayani.

“Kwamishinan ‘yan sanda ya ce a sanya lokaci Umar Farouk Musa ya zo. Sau hudu ana sa rana da lokaci, ni ina zuwa, amma Umar Farouk Musa bai zuwa.

“Don haka a ranar 8/11/2021 na debi ma’aikata muka je ginin da Vision FM Kaduna ke a cikin na fara kware kwano da balle kafofi, saboda ina son in yi gyara. In sake wa ginin sabon fasali.

“Duk abin da na yi ban saba wa doka ba. Don Vision FM kyauta suke zaune a gidana ba haya suke ba. A doka lokacin da ya yi mani kawai zan ba su su tashi. In haya suke biya, wannan kuma akwai tsarin da doka ta bayar.

“Ban je kotu ba, domin abin da Umar Faruk Musa ke so ke nan, mu je kotu a yi ta jayayya suna zaune a cikin gidan. In na amshi gidana, in sune ke da bukatar zuwa kotu, to su tafi, mu kuma zuba shari’a.

“Ga takardun duk da muka yi musaya da gidan rediyon na vision FM wadanda duk Umar Faruk Musa ya sanya wa hannu da wadanda na rubuta na sanya ma hannu.

“Wannan shi ne tsakanina da gidan rediyon Vision FM, Kaduna.”
Tare da labarin nan akwai duk takardun da akayi musaya.tsakanin vision FM Kaduna da kamfanin dialogue computers mallakin mahadi shehu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here