AN FARA SHARI’AR SHITTU S. SHITTU DA GWAMNATIN TARAYYA

0
64

AN FARA SHARI’AR SHITTU S. SHITTU DA GWAMNATIN TARAYYA

Mu’azu Hassan
@Katsina City News

A yau Alhamis 11/11/2021 aka fara Shari’a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kamfanin motoci na MASLAHA da Shittu S. Shittu da Muhammad S. Shittu da kuma Aliyu Lawal, wanda ake kira Tito.
Shitu s shittu shine tsohon shugaban jam iyyar APC na jahar katsina yanzu kuma sakataren jam iyyar na jahar katsina.

An yi zaman ne a babbar kotun Gwamnatin Tarayya da ke kallon filin wasa na Muhammadu Dikko.

An fara zaman ne da karfe 9.30 na safe, inda Alkalin ya shigo dakin Shari’ar, kuma aka kira karar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kamfanin MASLAHA MOTORS, Shittu S. Shittu, Muhammad Shittu, sai Aliyu Lawal, wanda ake kira Tito.

Lauyar masu shigar da kara wato Hukumar Kwastam mai suna Barista A’isha Muhammad ta tashi ta gabatar da kanta a kan tana tsayawa wa Hukumar Kwastam.

An kira daya daga cikin wadanda ake kara Lawal Aliyu Tito, wanda ya shiga akurkin wadanda ake zargi.

Daga nan Lauyoyi biyu; Barista I. K. Shebron da kuma T. Anjob, suka mike suka gabatar da kansu a matsayin wadanda ke tsaya wa Aliyu Lawal Tito.

Lauyar wadanda suka shigar da kara sun yi bayanin cewa, sun ba da takardun gayyatar zuwa kotu ga kamfanin MASLAHA. Sannan wanda ake tuhuma na uku; Muhammad Shittu yana karkashin beli ne, amma wanda ake tuhuma na biyu Shittu S. Shittu, sun kasa samun sa, balle su ba shi takardar gayyata zuwa kotu, amma wanda ake tuhuma na hudu, Aliyu Lawal Tito ya zo kotu tare da Lauyoyinsa.

A kotun babu Lauyoyin MASLAHA MOTORS, Shittu S. Shittu da kuma Muhammadu Shittu, kuma su ma ba su zo da kansu ba.

Lauyar masu shigar da karar ta nemi a dage Shari’ar zuwa wata ranar domin su tabbatar kafin lokacin sun tattaro duk wadanda ake zargi gaba daya su kuma gabatar da su a gaban kotu.

Bayan tattauna rana tsakanin Lauyoyin Aliyu Lawal da ma’aikatan kotu, an tsayar da ranar 9 ga Disamba a matsayin ranar da za a ci gaba da Shari’ar.

Da yake ba a karanta tuhumar da ake wa wadanda ake zargi ba tun da babu uku cikin hudu da ake tuhumar, ba mu iya samun bayanin zarge-zarge da tuhume-tuhumen da ake masu ba.

Amma dai karar Hukumar Kwastam ce ta shigar da ita a madadin gwamnatin Tarayya a kan kamfanin MASLAHA MOTORS, Shittu S. Shittu, Muhammadu Shittu da kuma wani jami’in Kwastam mai suna Aliyu Lawal Tito.

Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
www.thelinksnews.com
07043777779 081377777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here