Majalisar Malaman Indonesia ta haramta kuɗin crypto da tallar kudin a matsayin haja.

0

Majalisar Malaman Indonesia ta haramta kuɗin crypto da tallar kudin a matsayin haja.

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Majalisar malamai ta Indonesia ta yanke hukuncin cewa amfani da kuɗin intanet na crypto a matsayin hanyar ciniki, haramun ne a Musulunci, amma ta ce ana iya kasuwancin ƙadarorin da suka shafi intanet, kamar yadda ɗaya daga cikin shugabanninta ya bayyana.

Indonesia, ƙasa mafi yawan musulmi a duniya, ta haramta amfani da crypto a matsayin kuɗi, amma ta ce ana iya saka hannun jari da kasuwancin kayayyaki na intanet a kasuwar sayar da kayyaki.

A matsayin hanyar biyan kuɗi, an haramta amfani da kuɗin crypto bisa tsarin dokar shari’ar musulunci saboda suna dauke da abubuwa na rashin tabbas da cutarwa, kuma sun saɓa wa dokokin ƙasa, kamar yadda Asrorun Niam Sholeh, shugaban majalisar malaman ta MUI ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters.

See also  Bikin Naɗin Garkuwar Kabin Argungu Ya Ƙayatar Da Al'ummar Ƙasarnan

Sannan majalisar ta ce tallar kuɗin crypto a matsayin haja haramun ne, inda majalisar malaman ta kamanta kuɗin da caca, saboda bai cika sharuɗɗan shari’ar Musulunci kamar kayayyi da kuma tsabar kuɗi da za a iya gani da sauransu ba.

Amma majalisar ta amince a yi kasuwancin kuɗin ta hanyar da bai saɓa wa shari’a ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here