Kamfanin Coca-Cola Ya Maka Pop-cola Kara A Gaban Kotu

0

Kamfanin Coca-Cola Ya Maka Pop-cola Kara A Gaban Kotu

Kamfanin lemon Coca-Cola ya shigar da karar kamfanin Mamuda Beverages Nigeria Limited, wanda suke samar da lemon Pop-cola a gaban babban kotun tarayya dake Kano, bisa zargin amfani da wasu launukan kasuwancinsu, kuma hakan yana rikitar da masu siya, kamar yadda kamfanin Coca-Cola yayi zargi, tare da cewar sune suka fara saka sunan kamfaninsu ‘coca-cola’ a kasar nan Nigeria da sauran kasashen ketare.

Majiyar Nasara Radio (Amanar Talaka) ta rawaito cewa, lauyan dake kare bangaren da ake kara, ya bukaci kotu ta basu lokaci domin zuwar mata da hujjoji da zasu gamsar, nan take Alkalin babbar kotun, Jostis Muhammad Nasir Yunusa, ya dage zaman har zuwa ranar 11 ga watan Disambar shekarar nan da muke ciki ta 2021, domin sauraron kowanne bangare.

A watan shida (June) na wannan shekarar ne dai aka kaddamar da lemon na Pop-cola, wanda kamfanin Mamuda Beverages Nigeria Limited ke sarrafa shi, lemon da mutane da dama suka karbe shi hannu biyu, ciki harda gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Mun dauko daga shafin hantsi news na Facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here