AN BIYA DUK KANSILOLI DA CIYAMOMIN DA AKA RUSA KUDADEN SU….inji Alhaji Bature Umar masari
Daga
Muhammad danjuma
@ katsina city news
Gwamnatin katsina ta biya duk ciyamomi da kansilolin da aka rusa kudaden su kamar yadda hukuncin babbar kotun tarayya tace inji Alhaji bature Umar masari shugaban kwamitin tabbatar da biyan da gwamnatin katsina ta kafa.
Bature masari ya bayyana haka a wata tattaunawar musamman da babban editan jaridun katsina city news yayi dashi a ofishin sa.
Yace zababbun da biyan ya shafa sune,ciyamomin kananan hukumomi talatin da hudu.mataimakan su 34.sai kansiloli 361 sune ya bayar da jumla 429.
An biya su kudaden albashin su.wanda dukkanin su ya kama naira bilyan 1,539,481,047, sai kudin sallama na gama aiki Wanda ya kama naira milyan dari hudu da saba in da tara .475,899,414. Jumlar kudaden da aka biya naira bilyan biyu da dori lissafin ya kama haka.2,015,380,461.
Masari, yace akwai mutane sittin da hudu wadanda aka tabbatar da cewa kudin da aka biya su basu cika ba.don haka za a kara masu
Su kuma an lissafa kudin da za a cika masu shine milyan ar ba in da takwas da doriya.
Yanzu an gama tantance wadannan mutane 64 da abin da ya kamata a cika masu.yanzu sune za a biya nan bada jimawa ba.
Bature masari,yace kwamitin shi ya bi hukuncin babbar kotun filla filla da umurnin da ta bayar kuma, mai girma gwamna yace ayi aiki dashi.
Yace hatta biyan kudin mun biya kafin wa adin da babbar kotu ta bayar ya cika.
Matsalar wasu da aka rage masu wajen biya .kuskuren lissafi ne kuma an gyara za a cika ma duk wadanda abin ya shafa kudaden su.
Masari yace hukuncin biyan kudaden bai shafi sakatarori ba,da kuma kansilolin da suke ba zababbu ba.domin su kujerar su ta nadi ce.kuma hukuncin kotun bai shafe su ba.
Masari, yace sun yi amfani da doka hudu wajen biyan kowa hakkin shi kamar yadda ta kama.
Na farko akwai dokar kasa da ta raba albashin duk wani da aka zaba kujerar ta siyasa. Wannan dokar ta fayyace nawa za a biya ciyaman da sauran zababbu.
Doka ta biyu ta jahar katsina ta shekarar 2007 wadda ta fayyace albashin ciyaman da sauran zababbu a kananan hukumomi.
Da kuma dokar 2009.wadda aka gyara duk akan albashin zababbun shugabannin kananan hukumomi a jahar katsina.
Sannan akwai takardar da aka rika biyansu kudaden su lokacin suna mulki kafin a rusa.rekod din yana nan.
Bature masari yace da wadannan hujjojin mukayi amfani muka kididdige kudin kowa muka biya shi.
Ya kara da cewa, mun biya kudin a matakai uku.biyan farko zuwa na uku na karshe.kuma kowane mai hakki shine ya bayar da asusun ajiyar da za a zuba masa kudin shi.ta haka muka ba kowa.babu Wanda muka dau kudi muka bashi hannu da hannu.
Bature masari, yace duk matakan biyan da halin da ake ciki gwamnatin katsina ta sanar da babbar kotun tarayya, kamar yadda ta ummarta kuma akayi aiki da hukuncinta Kafin lokacin da ta bayar ya kammala.
Kudaden sun kama na tsawon watanni Goma sha hudu da kwanaki ashirin da suka rage masu ne bisa kujerar zabarsu kamar yadda hukuncin kotun ya fada
Katsina city news ta gano wasu
Zababbu 174 sunyi wani zama da shugabannin jam’iyyar PDP da wasu lauyoyi suna korafin wai biyan da akayi masu kamar akwai coge.sun amince an biyasu sun amshi kudin amma akwai coge.a ganin su.kuma har sun rubuta ma babbar kotun kasa korafin haka.
Amma takardun da jaridun taskar labarai ta gani wadanda dasu aka dogara akayi biyan.kamar ana son kawo siyasa a biyan kudaden da zababbun suka amsa.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245