Gwamnatin Kaduna za ta kori malaman makaranta 233

0

Gwamnatin Kaduna za ta kori malaman makaranta 233

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Hukumar ilimin bai-ɗaya ta jihar Kaduna za ta kori malamai 233 da ake zargi sun gabatar da takardun makaranta na bogi.

A cikin jawabin shugaban hukumar Tijjani Abdullahi da gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya wallafa a Facebook ya ce an tantance takardun malamai 451 ta hanyar tuntuɓar makarantun da malaman suka yi iƙirarin sun yi.

Shugaban ya ce bahasin da makarantu 13 suka bayar ya nuna malamai 233 takardun jabu suka gabatar.

Ya ce ɗaya daga cikin makarantar da aka tura wa takardun malaman ta nesanta kanta da shedar karatu 212 daga cikin 233.

“Don haka hukumar za ta kori malamai 233 da suka gabatar da takardun makaranta na jabu kuma za a gabatar da takardunsu ga ma’aikatar shari’a domin fuskantar hukunci. “

Hukumar ta ce za ta ci gaba da tantance sahihanci takardun malaman jihar a matsayin ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin Kaduna ke ɗauka da farfaɗo da ilimi.

Hukumar ta kuma ce za ta yi wa malaman jihar 12,254 jarabawar gwaji da horo wanda za a fara daga watan Janairun 2022

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here