Shugaban kamfanin Tiwita Jack Dorsey ya yi murabus

0

Shugaban kamfanin Tiwita Jack Dorsey ya yi murabus

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Shugaban lkamfanin Tiwita Jack Dorsey ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, inda wani babban jami’in kamfanin Parag Agrawal ne zai maye gurbin Mista Jack.

Mista Dorsey, wanda ya kirkiri shafin na sada zumunta a shekarar 2006, shi ke jan ragamar Tiwita tun daga wancan lokacin.

A wata sanarwa da ya fitar, Jack ya ce “lokaci ya yi da ya kamata na kauce,” tare da cewa kamfanin zai ci gaba da gudana.

Ya kara da cewa ya amince da kwarewar wanda zai maye gurbinsa a matsayin shugaba, tare da mika sakon godiya gare shi, ya kumna karkare da cewa ”Lokaci ya yi da zai jagoranci kamfanin.”

A shekarar 2011 ne Mista Agrawal ya fara aiki da Tiwita, kuma tun shekarar 2017 ya ke jagoranbtar fannin fasahar kamfanin.

Mista Dorsey dai ya dade ya na fuskantar matsin lamba, daga masu zuba jari kan ya sauka daga mukaminsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here