Takaitaccen Tarihin Rayuwar Marigayi Dr. Rabe Nasir.
An haifi Hon. Dr. Rabe Nasir ne a ranar 1 ga watan 10 na shekarar 1960 a garin Mani da ke jihar Katsina.
Ya halarci makarantar Central primary school da ke Mani a tsakanin shekarar 1968 zuwa 1975.
Daga nan sai ya wuce zuwa Makarantar Gwamnati da ke Giwa da ke yankin Zaria daga shekarar 1975 zuwa 1980 inda ya samu sakamakon kammala makaranta na Africa ta yamma wato WAEC.
A shekarar 1981 Dr. Rabe Nasir ya samu admission a Jami’ar Bayero ta Kano inda ya karanta fannin kimiyyar Siyasa wato (POLITICAL SCIENCE) inda ya kammala a shekarar 1984.
A shekarar 1996 Dr. Rabe Nasir ya samu gurbin Karo ilmi a Jami’ar Abuja inda ya yi Digirinsa na na biyu wato (INTERNATIONAL RELATION).
Dr. Rabe Nasir ya ta6a zama Dan majalissar wakilai da ya wakilci kananan hukumomin Bindawa da Mani a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
A shekarar 2015 ne Gwamna Aminu Bello Masari ya nadashi ya nadashi a matsayin SA a 6angaren kimiyya da Fasaha.
A shekarar 2019 Kuma aka sake nadashi a matsayin sabon kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Katsina.
Dr. Rabe Nasir ya kasance mutumin kirki Gogaggen Dan siyasa Kuma Haziki a fannoni Daban-daban.
Dr. Rabe Nasir ya rasu ya na da shekaru 61 a Duniya bayan da wasu marassa Imani su ka hallakashi a gidanshi da ke Katsina.
Allah ya jikansa da Rahama ya kyautata makwancinsa ya haskaka Kabarinsa.