DA DUMI DUMINSU: Senata Orji Uzor Kalu Mai Wakiltar Abia Ta Arewa Ya Saka Gasar A Shafinsa Na Kafar Sada Zumunta Watau Facebook.
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Sanata Orji Uzor Kalu Yasaka wannan gasar da misalin karfe 10:00am na safiyar yau asabar bayan ya kammala atisaye na motsa jika a cikin gidansa.
Duk wanda yasamu damar rubuta sunan Sanata kamar haka Sanata Orji Uzor Kalu a jere babu wanda yashiga tsakani zai bashi kyauta.
Duk wanda yasamu wannan nasara yahada da lambar account dinshi, saidai al’umma dayawa sun samu cin wannan gasa.