AIKIN JARIDA BA LAIFI BANE

0

AIKIN JARIDA BA LAIFI BANE

In ji Muhammad Danjuma

Shugaban kamfanin Matasa Media Links da ke Katsina, masu buga jaridun jaridar Taskar Labarai, The Links News da kuma Katsina City News da ke yanar gizo da mujjalar Katsina City News da ke fitowa lokaci-lokaci don ba da labaran tarihin Jihar Katsina da al’amuran yau da kullum, Muhammad Danjuma Katsina, ya ce, aikin jarida ba aikata laifi bane, ba kuma abin tsana, kyara, ko tsangwama ba ne.

Danjuma, wanda yake magana a taron sanin makamar aiki na wuni daya da ya shirya wa ma’aiktan kamfaninsa da kuma wakilan sabbin dauka, wadanda za su rika aiko rubutu daga Kananan Hukumomi da Jihohi guda uku da suke makwabta ka da Jihar Katsina, ya tabbatar da cewa aiki jarida, aiki ne mai daraja, kuma Dodo ne ga azzalumai da masu mugun nufi.

“Dan jarida bai fi karfin doka ba, bai kuma fi karfin wani ibtilai ko ajizanci ya same shi ba”, in ji Danjuma.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka a kiyasi sama da ‘yan jarida 100 ke tsare a gidajen yari daban-daban a duniya ciki har da Nijeriya.

“An kashe da yawa, wasu an nakasa su, wasu an masu tarko, wasu gadar zare aka shirya masu suka fada, aka kule bakinsu. Don haka taka tsantsan ga Dan jarida wajibi ne”, ya jaddada.

Danjuma ya kara da cewa; “Ku sani su ma ‘yan jarida mutane ne, kuma ‘yan kasa, duk wanda yake neman zaluntarsu a kan aikinsu, za su iya neman hakkinsu a kotuna da kai korafi a hukumomin tsaro.

“Kwanan nan kun ji yadda kotu a Jihar Kano ta tilasta wa Gwamnan Kano ya biya Jafar Jafar diyyar Naira Dubu 800 a kan bata masa lokaci da ya yi. An biya Dan jaridar kudin har ya ba da su ga wani gidan rediyo a taimaka wa marasa lafiya.

“A nan Katsina akwai kes din Mazoji da Matazu, ko da yake ba na jarida bane, amma misali ne na yadda in aka zalunce ka za ka iya neman kotu ta bi maka hakkinka.

“Mazoji ya nemi kotu ta fitar masa hakkkinsa a kan Matazu, kotun farko ta ce a biya shi Naira miliyan tara da wasu daruruwa. Kotun daukaka kara ma ta jaddadda hukuncin, yanzu maganar na Babbar Kotun Kasa”, ya bayyana.

Danjuma ya ce; “Ku je ku yi aikin a tsanake bisa doka da ka’idar aiki, ba wanda ya isa ya hana ku, ko ya takura maku. Ku sani makiyanku da aikinku suna nan suna jira kuskure, ko ajizancinku, don su yi amfani da shi a kanku. Don haka ku bude ido da taka-tsantsan”.

See also  Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro 

Ya kara da cewa, aikin jarida kamar wani wasa ne a kasar Hausa, wanda ake cewa ga na tsiya, ga na arziki. Duk wanda ka dauka sai a yi maka shi.

Ya ce a jarida akwai bincike, akwai rahoto, wanda yake kala-kala ne, akwai nazari akwai sharhi.

“Mun iya jaridar wayar da kan jama’a, mun iya ta fadakarwa, mun iya ta ilmantarwa, mun iya ta kwatar ‘yanci, mun kuma iya ta sunkuru da sari ka noke.
Duk wanda ake so mun iya. Kuma su muke koya maku”, in ji Danjuma.

Kazalika ya ce; “Kun ji dadi, wanda yanzu in yanayi ya canza ana son canza salon jaridar, sai kawai a canza maka gari ko kasa ka yi ta aikin ka, wanda yanzu ‘yan jarida da yawa na gudun hijira, suna kuma aikinsu daga can. Misali Jafar Jafar yana London. Duk inda muka ji ba mu da aminci sai mu matsa mu kuma yi aikinmu. A baya babu wannan damar”.
Ni inji danjuma nayi jaridar sunkuru har sau uku kuma Allah ya tsare muka fita, biyu zamanin soja daya fara hula ko yanzu ta baci muna iya komawa ..inji shi

Danjuma ya kara da cewa; “Mai kaunarmu, mun san shi. Wanda ya raga mana, mun sani. Wanda yake taimakon mu, mun sani. Mai hakuri da mu, mun sani.

“Duk wanda ya cutar da mu, mu ma za mu jira shi, kuma in Allah ya so zai fado mana a tsanake, sai mu yi masa aiki bisa daidai, ” in ji shi.

Danjuma ya shaida wa ma’aikatan cewa; “Tsarin jaridunmu, kullum muna cikin shirin ko-ta-kwana ne, za kuma mu iya canzawa cikin lokaci kankane mu ci gaba da aiki irin yadda yanayi ya zo da shi.

“Wani masanin fasahar yaki yana cewa, in kana son ka zauna lafiya, to ka yi shirin yaki. Dan jarida ya fi kowa son zaman lafiya, ya kuma yi aiki a kan haka, amma kullum ya rika tanadar kayan yaki.

“Duk wanda ya cutar da mu, shi ma ya jira sa’ar da Allah zai kawo mana a kansa”, ya karkare.
Wakilan sun samu horo na yadda zasu kiyaye dokokin aikin da kuma yadda zasu kare dokokin kasa a wajen aikin su.
Da yadda zasu yi amfani da kalmomi marasa illa a rubutun su.da yadda zasu taimaki kasar mu da yankin arewa baki daya da jahar mu.
@ katsina city news
Www.katsinacitynews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here