FADAN CIKIN GIDA NA RURUWA A TSAKANIN BARAYIN DAJI A YANKIN BATSARI

0

FADAN CIKIN GIDA NA RURUWA A TSAKANIN BARAYIN DAJI A YANKIN BATSARI

Daga wakilanmu
@ katsina City News

Wani fadan cikin gida yana ta ruruwa a tsakanin barayin daji na yankin Batsari da kuma abokan ta’addacinsu daga bangaren Jihar Zamfara.

Wata majiya ta tabbatar mana cewa barayin daji na yankin Batsari yanzu suna auka wa duk bakon barawon da suka gani ya fito daga yankin Zamfara, ko kuma yaran Dangote, wanda ke da iyaka da Jibia da kuma Zamfara.

Majiyar ta ce, dan fashin nan mai suna Abu Radda, wanda yankunan da ke karkashin, sun kama da Nahuta, Madogara, Zamfarawa, Tashar Modibbo da wasu kananan garuruwa.

Ya umurci yaransa su kama duk wani bakon barawo da suka gani.

Haka nan shi ma dan ta’addar nan mai suna Abdu Mai Komi, wanda ke da yankunan da yake iko da su kamar Gobirawa, Garin Runji, Garin Yara, Kondatso da kuma Yasure.

Shi ma ya hada kai da Abu Radda a kan kai hari ga duk wani bakon barawo da suka gani.

Majiyarmu ta ce harin da aka kai kwanakin baya a garin barawa ta Karamar Hukumar Batagarawa kusa da birnin Katsina.

Yaran Dangote ne suka kai shi karkashin wani Kwamandansa mai suna Sale mai linzami.

Majiyar ta ce an kai harin ne don kwasar abinci da dabbobi.

Amma bayan maharan sun gama ta’addacinsu a garin Barawa a hanyarsu ta komawa sansani Dangote da ke dajin Shimfida, yaran Abu Radda da na Abdu Mai Komai suka yi masu kwanton bauna suka kwace duk dabbobin, suka kashe wasu daga cikinsu, wasu kuma da kyar suka sha.

Majiyarmu ta ce kauyukan da ke yankin Ruma Tsohuwa, sun ga yadda aka yi wannan fadan.

Majiyarmu ta ce bayan sun kwace dabbobin da makaman da suka kwata, sun raba a tsakaninsu da wasu barayin da suka taimaka masu.

Majiyarmu ta ce fadan ya kazanta da har wasu manyan Kwamandojin Dangote sun canza mazauni sun sake komawa cikin daji sosai.

Majiyarmu ta ce Abdu Lankai da Ilyan Marke, duk sun canza mazauni daga inda suke a da.

Majiyarmu ta ce wannan fadan ya jawo yanzu kowane bangare ba ya yawo da bindiga saboda tsoron kar in dayan bangaren ya gan shi zai masa lahani, ya kuma kwace bindigar.

Majiyarmu ta ce barayin bangaren Batsari suna so ne a kyale su su kula da yankinasu, su tsara yadda za su tafiyar da inda suke, ba sa son barayin Zamfara su rika shigar masu iyaka.

Mai ba mu labari ya ce a fadan yanzu ana kwarar yaran Dangote ne, kuma har ta kai ga ya ja baya, amma ana tsoron ya yi shiri ya dawo.

Mun tuntubi Kakakin Rundunar ‘yan sanda domin jin ta bakinsa, inda ya amsa mana, kuma ya ce zai bincika, amma zuwa fitowar rahoton nan, ba mu ji komai daga gare shi ba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08377777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here