DAN FASHIN DAJI YA NEMI AYI MASU ADDU’A

0

DAN FASHIN DAJI YA NEMI AYI MASU ADDU’A
Misbahu A batsari
@ katsina city news
Wani kasungumin Dan fashin Daji Wanda yake da barayi masu yawa karkashinsa.kuma yana da bindigu iyakar nasa, ya shiga wani gari( mun sakaya sunan garin) ya Nemi a Kira masa babban limamin garin.
Duk garin, an San ko waye shi.don haka da farko da mutane suka ganshi da yaran shi,har sun fara gudu, sai yace kar Wanda ya ruga .liman kawai yake son ganawa dashi .
Da aka Kira liman, sai Dan fashin yace addu a nake son ka tara mutane suyi mana,akan Allah ya kawo karshen wannan ta addacin da suke yi, kuma ana yi masu .
Dan fashin ya kawo kudi ya bada yace ayi sadaka.ya kuma kawo Rago, yace a yanka ayi sadaka.
Yace wannan lamarin ya ishe su.
Mun tabbatar da labarin nan ta magana da liman din da abin ya faru da kuma mutanen gari da suka shaida.amma mun sakaya sunan garin Dana limamin saboda tsaron lafiyarsu. Lamarin ya faru ne a karamar hukumar batsari.
Wani binciken da muka tabbatar shine toshe layin waya,bai yi ma barayin daji wata illa ba can can.
Abin da ya fi kuntata masu shine rashin shigar da man fetur da kuma abinci.
Wannan yafi cutar dasu sosai.kuma shine yafi basu azaba.amma waya sukan hau tsaunuka suyi magana da duk inda suke bukata.
Rashin waya yafi cutar da munafukai masu buga waya su basu labari.amma basu dake a cikin daji ba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here