Allah Ya yi wa Sani Garba SK rasuwa a Jiya

0

Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a jiya Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Wani fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ɗan wasan.

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.

“Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin,” in ji Amart.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here