An kama wani shugaban addinin Hindu mai tsaurin ra’ayi, Kalicharan Maharaj,

0

An kama wani shugaban addinin Hindu mai tsaurin ra’ayi, Kalicharan Maharaj, a tsakiyar Indiya saboda yin kalaman ɓatanci ga shugaban ƴancin kai na kasar Mahatma Gandhi.

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan yin jawabi a wani taro inda ya yaba wa mai tsatsauran ra’ayin Hindu da ya harbe Gandhi a shekarar 1948, watanni bayan da Indiya ta sami ƴancin kai daga Birtaniya.

Mahatma Gandhi mutum ne mai daraja a Indiya. Amma wani sashe na masu tsatsauran ra’ayin addinin Hindu na da’awar cewa jagoran ƴancin kai ya fi fifita Musulmi.

Sun sha bayyana wanda ya kashe shi a matsayin mai kishi.

See also  Asibitin Dubai zai raba tagwayen Najeriya da suka hade a kyauta

Haka kuma shugaban addinin na Hindu Kalicharan Maharaj ya caccaki addinin Islama a cikin jawabinsa.

Jawabinsa na zuwa kwanaki bayan wasu shugabannin Hindu masu faɗa a arewacin jihar Uttarakhand sun fito fili sun yi kiran farwa musulmi.

Sharhin Jaridu da dama sun yi kira ga Firaminista Narendra Modi da sauran shugabanni na jam’iyyar BJP mai mulki su fito su yi Allah wadai da jawaban. Har yanzu Mista Modi bai ce komi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here