AN SACE KANWAR SANATAN BAUCHI
Ranar laraba da dare wasu yan bindiga sun kai hari garin Tilden Fulani Toro LGA inda suka yi awon gaba da wata matar aure mai suna Asabe wacce ake zaton kanwace ga Sanata Lawan Yahaya Gumau mai wakiltar Bauchi ta kudu a majalisar dattijan Nigeria.
Maharan sun rikita garin da harbe harbe daga nan suka shiga gidan matar suka fito da ita har yau babu labari. Saiko wasu mazauna garin na zaton akwai hadin bakin wasu matasa bata gari da ake zargi, saboda a kwanakin bayama an kai irin wannan hari an kashe wani dan kasuwa mai sayar da magunguna.
Dukkan kokarin da muka yi don ji daga bakikin kakakin yansanda SP Mohammed Ahmed wakil ya ci tura, amma duk lokacin da muka samu ji daga gareshi za mu sanar da ku.
Daga Muazu Hardawa, Edita Alheri.