Motarmu Ta Lalace Akan Hanyarmu Ta Zuwa Makaranta

0

Motarmu Ta Lalace Akan Hanyarmu Ta Zuwa Makaranta

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Wasu dalibai su uku-3 sunki halartar zana jarabawa sakamakon basuyi karatun komaiba. Sun shirya ma Malan karya cewa sun halarci taron bikin daurin Aure, kan hanyarsu ta dawowa motarsu ta lalace kamar yadda kuke gani

Anyi sa’a Malamin yanada fahimta sai yabasu kwana uku-3 yace mu shirya zai zana musu tasu jarabawar, bayan kwana uku suka shirya tsaf suka samu Malamin sukace masa sun shirya shikadai suke jira

Mal, ya yanke shawarar ya ajiyesu a aji daban-daban tareda tambayoyi hudu kachal dake rubuce cikin takarda kamar haka.

Tambaya ta farko dake rubuce cikin takarda jarabawar itace
1: Sunan Wanda Yayi Auren? (25-Marks)
2: A Ina aka daura Auren? (25-Marks)
3: A Ina Motar taku ta lalace? (25-Marks)
4: Wace irin motace kukaje da’ita ta lalace? (25-Marks)

See also  MAGANIN CIWON SANYI NA MATA DA MAZA

Kuma dukkaninsu anasan subada amsa iri daya.

Yanzu haka da muke maganar suna cikin dakin zana wannan jarabawa

Masu karatu mezakuce???

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here