RUGA KACHALLA NA NAN DA RANSA.

0

HARIN JIRGIN SAMA A ZAMFARA DA SAFANA AKAN YAN TA ADDA
…….RUGA KACHALLA NA NAN DA RANSA..
@ katsina city news
Daya daga cikin yan ta addar da aka ruwaito jirgin sama ya kashe a harin da ya kai a yankin zamfara Wanda yayi sanadin kisan Alhaji auta shine Ruga kacalla,kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito
Binciken jaridun katsina city news a dajin safana inda ruga kacalla keda karfi ya tabbatar mana ruga kacalla yana nan da ransa.


Haka Alhaji muhigge Wanda shine babban yaron Alhaji dan auta a yankin safana shima yana nan da ransa.
Majiyarmu ta tabbatar mana, bayan Harin da ya kashe Alhaji Dan auta.barayin daji sun shirya yi masa Jana iza ta alfarma.wanda aka gayyaci duk yan ta adda daga duk yankin katsina,zamfara,da sokoto da kaduna
Majiyarmu tace ana cikin Jana izar sai jirgin sama ya sake kai Hari na biyu inda ya kashe barayin dajin masu yawan gaske .
Majiyarmu tace ruga kacalla na safana da Alhaji muhigge sunyi niyyar zuwa Jana izar.amma basu je ba.wannan ne ya tseratar dasu.
Amma jirgin na yaki ya kai wani Hari a yankin safana ta jahar katsina a tsakanin daren jumma a da asabar Wanda yayi sanadin mutuwar wasu barayin na daji ciki harda manyan yaran ruga kacalla.
Alhaji Dan auta Wanda jirgin yaki ya kashe yana da yara a yankin zamfara da katsina da sokoto. Sai dai yana cikin barayin daji masu wayewa da saukin kai a duk yankin.
Kwanan ya gayyaci wani Dan jarida ba amurke yaje har tsakiyar dabar sa dake tsakanin katsina,zamfara da Kaduna.
Dan auta,bai amince wani barawo ya shigo masa yanki ba.bai da hali na kisan kiyashi kamar turji.ko Dan karami.
Kisan shi yanzu zai tarwatsa rundunarshi.kamar yadda yaran Buharin daji suka zama bayan an kashe shi.
Barayin daji basu da tsarin wani ya hau shugabanci in an kashe babban su.
In babba ya mutu sai dabar ta zama kowane mai karfi yaja nashi
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here