Jam’iyyar APC Tayi Babban Kamu A Jihar Kebbi.
Daga: Comrade Musa Garba Augie
Alh, Umar Isah Mungadi, Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi. Ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki APC. Hon, Umar Isah Mungadi Muna maka barka da zuwa jam’iyyar APC jam’iyyar mai adalci, gaskiya, da rikon amana.
Atareda damu akwai manyan jigagan jam’iyyar APC Kamar. DR, Hussaini Suleiman Kangiwa (“Sarkin Arawan Kabi”) Abdullahi Hassan Suru (“Garkuwan Suru”) San, Abubakar Chika Malami, Ministan Shari’a da sauran manya-manyan baki waɗanɗa suka samu halartar wannan taro.
Jagoran Siyasar jihar Kebbi Dr, Hussaini Suleiman Kangiwa (“Sarkin Arawan Kabi”) Yayi farin cikin ganin yadda al’umma suke tururuwa wajen shiga jam’iyyar APC Sarkin Arawan Kabi yayi Addu’a Allah yaba ƙasarmu lafiya da zaman lafiya baki daya