WA YA CI AMANAR WANI? TSAKANIN GWAMNA MASARI DA SANATA BABBA KAITA (1)

0

WA YA CI AMANAR WANI?
TSAKANIN GWAMNA MASARI DA SANATA BABBA KAITA (1)
…Asalin haduwar siyasar su
Mu’azu Hassan
@Katsina City News

A karshen shekarar 2009 ne, an kafa jam’iyyar CPC daga cikin jiga-jigan da suka kafa ta a Nijeriya shi ne Aminu Bello Masari. Daga cikin wadanda suka yi aiki tukuru daga Katsina shi ne Ahmad Dangiwa kankia

Ahmad Babba Kaita a lokacin yana birnin Fatakwal yana harkokin kasuwancinsa. Sai ya yi niyyar shiga siyasa, ya dawo garinsu Kankia ya fara, tare da yin mubaya’a ga Ahmad Dangiwa, wanda ya zama ubangidansa a siyasance.

Babba Kaita ya zama dan siyasa, kuma mabiyin gidan siyasar Ahmad Dangiwa.

Dangiwa ne ya kai Babba Kaita wajen Masari Uban siyasar adawar Katsina a lokacin. Masari ya amshe shi hannu bibbiyu, kuma ya rika mu’amala da shi a matsayin ’yan gida daya a siyasarsu.

A zaben 2011, Dangiwa ya tsayar da Babba Kaita takarar Dan Majalisar Tarayya a Kankia da Kusada.

Rikici ya dabaibaye jam’iyyar CPC a tsakanin bangaren Lado Dan Marke da kuma bangaren Masari. Rikicin ya ci gaba har bayan zabe.

Dangiwa da Babba Kaita sun tsaya cak, bangaren Masari CPC suka yi kamfen a zabi jam’iyyarsu. Daga baya kotu ta yanke matsaya.

Bayan zabe aka yi ta shari’a a tsakanin bangarorin biyu na CPC, bangaren Masari da Lado.

Masari ya yi tsayin daka kan kotu sai ta yi adalci, tsohon Kakakin Majalisa ne ya san mutane. Daga karshe kotu ta ba bangaren Masari gaskiya, su Ahmad Babba suka tafi Majalisar Tarayya.
Masari na a majalisar ranar da aka rantsar dasu.

Duk tsawon shekarun da Babba Kaita ya yi a Majalisa tsakaninsa da Masari sai dai a hoto.

Da zaben 2015 ya zo, Masari ya sake dagewa sai an bar Ahmad Babba, duk da wasu sun taso suna neman a canza shi. Masari ya ce Ahmad na kokari a Majalisa, ya tsaya kai da fata a kan a bar shi ya ci gaba. Haka aka sake zaben Babba a 2015.

Allah ya yi wa Sanatan Daura, Mustafa Bukar rasuwa. Wasu suka fito daga kwaryar yankin Daura suna neman takara. Daya Dan Majalisar Tarayya ne, biyu kuma jami’ai ne a gwamnatin Masari.

Aka tafi zaben fitar da gwani, Alhaji Nasiru Sani Zangon Daura yana gaban Ahmad Babba nesa ba kusa ba. Daga a je Sallah a dawo, labarin ya canza. Sauran Kananan Hukumomin suka zabi Ahmad Babba. Da haka APC ta dauke shi a matsayin dan takararta.

Wannan ya ja wa Masari bakin jini ba karami ba a wajen wasu dattawan Daura da wani yanki na mutanenta. Akan yaki Sanya Ahmad babba ya janye ma Nasiru sani zangon Daura.
Matsalar da masari da gwamnatin sa ta gani akan haka,wani shafi mai bukatar rubutun kansa.

Aka zo babban zaben cike gurbi, sai zaben ya taso da kalubale ba kadan ba. Akwai fushin ’yan kwaryar Daura, Kananan Hukumomi shida.ga tasirin Majigiri a Mashi-Dutsi, ga kuma fushin wasu ga Ahmad Babba a Kusada da Kankia.

Zaben Ahmad Babba shi ne zabe mafi tsada da wahala da gwamnatin Katsina ta gani, kuma shi ne zabe mafi wahala da tsada a tarihin APC a Arewa maso Yamma.

Gwamnatin Katsina ta dake, amma da kyar aka ci zaben. Ahmad Babba ya zama Sanata.

A zaben 2019 wasu sun taso suna neman takarar a APC, amma Masari ya dage ko zaben fitar da gwani kar APC ta yi a yankin Daura. A haka Ahmad Babba ya sake darewa kujerar Sanata a karo na biyu.

Wace matsala ce ta faru? Matsala ce ta cikin gida wadda rashin fahimta ce ta faru tsakanin Dangiwa da Babba Kaita.

Gwamnan Katsina ya yi iyakar kokarin daidaita su, amma abin ya ci tura.

“Ka tambayi Shitu S. Shittu Sakataren jam’iyyar APC shaida ne a kan duk kokarin da aka yi”, in ji wani da yake ba mu labari.

Babba Kaita sai ya dauka Masari ya fi goyon bayan Dangiwa ne, don haka sai ya fara surutai a kan Masari da gwamnatinsa.

Lamarin ya kara kazamcewa ne a lokacin da wasu matasan ’yan siyasa suka muzanta Babba Kaita a Kankia, kamar yadda jaridar SAHARA REPORTERS ta ruwaito.

Wani rahoton ya ce an masa ihu, an keta masa riga, amma mutanen Sanata Babba Kaita sun karyata labarin keta riga a wata hira da jaridar TASKAR LABARAI ta yi da su.
Sai kuma abin da ya faru a fadar hakimin Mashi, wajen daurin aure, inda wasu matasa suka yi masa ihu, amma wata sanarwa da daya daga cikin masu gayyatar daurin auren ya fitar ta ce, wadanda suka yi ihun matasa ne da aka zo da su daga wajen mashi, amma ba Ryan mashi. ba ne.

Sanatan ya kara fusata ne bayan zaben shugabannin jam’iyyar APC da aka yi na Jiha, tun daga mazabar Unguwani zuwa Jiha, Ahmad Babba ba shi da kowa, wanda hakan ya mai da shi mara tasiri a tsarin shugabancin jam’iyyar.

Duk wanda ya san siyasa, ya san in dai ba sasanci aka yi ba, Ahmad babba ko Kansila bai iya samu a APC. Wannan na daga cikin abin da zai iya bata masa rai, ya kuma dugunzuma shi.
A tsarin siyasar cikin APC an ma shi mutuwar tsaye. Sai dai in an sake lale.ko kuma ya tafi wata jam iyyar.

An shigo shekarar fitar da ’yan takarkari, ga zaben kananan hukumomi gwamnatin katsina ta shelanta yin shi,Babba Kaita ya san bai da gurbin takara ko tsai da dan takara a jam’iyyar APC ta Jihar Katsina. Don haka akwai fushi da bacin rai, kuma komai na iya faruwa daga bangaren Sanata Ahmad Babba Kaita.

Katsina City News
@www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@www.thelinksnews.com
0704 377 7779, 0081 377 7245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here