MATASHIN DA KE DAUKO HOTUNAN MAZA DA MATA TSIRARA….
…Ya amshi kudin rufa asiri
“…Na dau mutane 10 hoto”
….ya dauko hotunan mahaifanta
Daga wakilanmu
Wannan labari ne na wani matashi da yake kawalcin ’yan mata zuwa ga maza, kuma yana kawalcin mata zuwa ga mata masu neman mata. Sannan ya rika hada baki da su suna dauko masa matan ko maza zindir yana masu barazanar zai yada a shafukan yanar gizo, ko kuma su ba shi kudi.
Jaridun KATSINA CITY NEWS sun gudanar da bincike a kan rayuwa da kuma aikin wannan matashin, wanda tuni ya fada komar jami’an tsaro suna bincike a kansa. Mun sakaya sunansa, mun kuma caccanza wasu bayanai da za su iya kawo cikas ga binciken da jami’an tsaro ke yi a kansa.
Yaro ne dan kasa da shekara 30, ya kammala karatunsa na gaba da Sakandare. Ya fito ne daga cikin kwayar Katsina.
Bayan ya gama karatunsa, sai ya fara sana’o’i daban-daban, ciki har da siyar da maganin kara lafiyar jiki da karfafa garkuwar jiki. Daga baya ya kara da sana’ar maganin karfin maza da karin ni’ima ga mata. Wannan ya ba shi damar sanin manyan mutane masu kudi, mulki da masu rike da mukaman siyasa da kuma manyan mata.
Dan gaye ne, wanda kullum yana cikin kwalliya. Wannan ya ba shi damar sanin ’yan mata ’yan kwalisa a cikin gari da makarantu.
Daga nan sai ya fara kawalcin hada kyawawan ’yan mata da kuma masu bukata. Yakan samu biyan kudinsa hawa biyu, duk abin da aka ba yarinya za ta ba shi wani kaso, wanda ya kai wa yarinyar shi ma zai ba shi abin hasafi.
A haka sai mummunan aikin nasa ya tumbatsa, ’yan mata da yawa suka san shi, kuma suna neman a hada su da mai kudi wanda za a yi harka da shi a samu kudi.
A bangaren mabukatan ma, kowa ya san shi a matsayin yaro ne wayayye da ke kawalcinsa a zamanance.
Zai turo maka hoton yarinya da bidiyonta, sai ta yi zai shiga tsakani. Sannan ta je inda aka tsara ta same ka.
Wayarsa tana da hotunan ’yan mata daban-daban da shiga kala-kala, wasu zindir haihuwar uwarsu don kawai a samo masu kwastomomi masu hannu da shuni.
Da tafiya ta yi tafiya, sai wasu manyan mata suka fara bukatar ya samo masu ’yan matan da za su yi harkar neman mata da su (madigo). Nan ma wata tsinanniyar kasuwar sai ta bude.
Don haka sai ya zama haramtattun kudin suna shigo masa ta hanyoyi biyu, ya kai ’yan mata ga maza, ya kai ’yan mata ga manyan mata.
Sai wata shawarar ta zo masa inda ya rika hada kai da matan suna dauko masa hotunan maza da matan da suke harka zindir.
Yarinya za ta dau hoton sai ta turo masa, sai ta goge hoton daga wayarta nan take. Da haka ya tara hotuna a wajensa masu yawan gaske. Nan ma sai wasu kudin shigar suka rika tudadowa.
Zai maka waya ya ce ga abin da yake da shi. Sai ka ga neman rufin asiri ya shiga. Sai maganar kudi ta ratso.
Idan yarinyar da yake wa kawalci ta kawo wasa, sai kawai ya rika yi mata barazana da hotunanta zigidir din da ke wajensa.
Binciken da muka yi a rayuwar wannan matashi mun gano yadda yake fantamawa da jin dadi, ashe da kazaman kudaden da yake samu na kawalci ne da barazanar bata suna.
A wayarsa, wadda jami’an tsaro suka bi, hotunan ’yan mata ne zindir da na wasu manyan mutane da ’yan mata suka dauka a sace da kuma mu’amala da wasu manyan matan da yake wa kawalcin ’yan mata don madigo.
Har zuwa rubuta wannan rahoton binciken yana ci gaba, yayin da jami’an tsaron da ke aikin suke ta tattara bayanai.
YADDA MUKE DAUKAR HOTUNAN MUTANE TSIRARA
Mun hadu da wata yarinya a wani wurin sirri kamar yadda ta zaba, kuma ta amince ta yi magana damu.
A ikirarinta ta tuba, kuma har ta yi tsarki za ta yi aure, ta bayyana mana cewa; “Na samu wanda ya san waye ni, kuma ya amince ya aure ni a yadda ya san ni, amma bayan na yi nadamar abin da na aikata a baya, kuma na tuba.
“Mazan da na dauka hoto sun fi 10, amma duk na goge hotunan. Da yawansu sun taimake ni a auren nan da zan yi yanzu,” in ji ta.
Da take amsa wata tambayar a kan yadda suke daukar hotonan, sai ta amsa da cewa; “Wajen cire kaya in za mu ba da kanmu, sai mu kunna kyamarar wayarmu, kuma mu saitata daidai inda muke son mu dauka. In mun dauka, sai mu cire inda ba mu bukata mu bar inda muke son amfani da shi. Wani lokaci kuma ana labari za mu rika yi kamar “chatin” ko “game” muke, amma bidiyon mutum muke dauka”.
Da wasu hanyoyin da yarinyar ta bayyana mana.
Ta ce a wayarta ta rage wasu hotunan da ta ce wani dalili ya sa za ta adana su ko da kuwa ta yi aure.
A bidiyon wani mutum ne zindir yana kidaya kudi zai ba wata yarinya kudi,wani bidiyon kuma wani mutum ne ke wanka.da dai wasu shafukan hotunan.masu tada hankali
A hirar da muka yi da ita ta ce wasu yan mata kowa suke dauka, wasu kuwa sai wadanda suka ci amanar su, ko suke neman cin amanar su, sai su dauka,a yi mutuwar kasko.
YADDA NA KWACI KAINA
Wani da ya yi ikirarin an taba daukar sa hoton, ya bayyana wa jaridunmu cewa; “Wata yarinya ce ta yaudare ni ta dauke ni hotuna, sai wata kawarta ta tabbatar mani ta ga hotunan da bidiyon a wayarta.
“Sai na yi amfani da kudi, ni ma na samo hotunan mahaifinta da mahaifiyarta da ya yayarta da wani wanta zindir haihuwar uwarsu.
Ya akayi? ” wannan kuma ba ruwanka” inji mutumin
Muka fara zaman, tana kallo na Biri, ina mata kallon Ayaba. Wata rana daga gardama sai ta turo mani hotunan. Ni ma sai na tura mata nawa. Sai dai na ji labarin tana asibiti kwance”.
Wannan shine rabuwarmu da ita.
Binciken jaridun KATSINA CITY NEWS, ya gano manema mata a wannan zamanin suna cikin tsaka mai wuya na hatsarin daukarsu zindir daga matan da suke nema.
Allah ya sawwaka, ya kiyaye.
Wakilanmu na musamman ne suka gudanar da wannan binciken.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai ,
@Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245