TARE HANYAR MANOMA DA MAKIYAYA: ..KIRA GA DAN MAJALISAR TARAYYA NA FUNTUA; MUNTARI DANDUTSE

0

TARE HANYAR MANOMA DA MAKIYAYA:
..KIRA GA DAN MAJALISAR TARAYYA NA FUNTUA; MUNTARI DANDUTSE
…Kafin ya zama wata fitina
Mahmood Hassan
@Katsina City News

A cikin watan Maris, 2021, Kungiyoyi guda uku, na Miyyati Allah, da masu noman rani, da kuma na manoma da masu kamun kifi na garin Dukke da ke Karamar Hukumar Funtua a Jihar Katsina, suka rubuta wata takardar korafi zuwa ga kwamitin da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa na daidaita manoma da masu kiwo don ya sanya baki a kan yadda Alhaji Muntari Dandutse Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Funtua da Dandume ya tare masu hanyar zuwa neman abincinsu daga wata gona da ya saya.

Takardar, wadda jaridun TASKAR LABARAI suka gani, an yi kwafinta ga Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, kuma tana da sa hannun Wakilan Kungiyoyin da suka yi koken.

A takardar sun yi korafin cewa Dan Majalisar ya toshe wata hanya da manoma da makiyaya ke bi sama da shekaru 70. Kuma wannan yanzu ya takura dimbin masu sana’ar da shi ne hanyar abincinsu da zuriyyarsu.
Suka ce wajen gona ce ake ratsawa, asalinta ta Marigayi Babajo Ibrahim ce, ya sayar wa Sani Idris Bagiwa, dukkanin su (Allah ji kan su da rahama), ba su toshe hanyar ta manoma da makiya ba.

Amma Muntari Dandutse yana siyen gonar, sai ya katange hanyar ya yi mata get ba yadda za su iya wucewa zuwa dam din Dukke da ke jikin gonar su yi noman rani, kiwo da kuma kamun kifi wanda suka saba tun iyaye da kakanni.

Yanzu tafiyar mintoci sai aka mayar masu da ita sai sun yi gewaye, wanda kan iya daukar su fiye da awa.

Takardar ta roki kwamitin ya sanya Dan Majalisar ya ji tausayin wannan al’ummar ya bude masu hanyar da suke bi suna sana’arsu sama da shekaru 70.

Hanyar da duk kwamitocin na tantancewa da tabbatar da hanyoyin makiyaya na kasa da Jiha sun san da ita, kuma sun tabbatar da ita.

Bayan kwamitin ya samu wannan wasika, nan da nan ya fara aikin sa, inda a ranar 24/3/21 aka fara zaman farko, tsakanin wadanda suka yi koken da jami’an tsaro da kuma wakilan wadanda ake korafi a kan sa wato Hon. Muntari Dandutse. Zaman an yi shi a fadar Sarkin Maska, Hakimin Funtua, Sambo Idris Sambo.

A zaman wakilai hudu daga masu koke wadanda suka fito daga Kungiyoyin da ke sana’a kusa da wannan Dam, sune Alhaji Hamza Dukke, Malam Tukur Bello, Alhaji Salisu Wakili, sai Ciyaman na Miyyati Allah na Karamar Hukumar Funtua.

Wadanda suka wakilci Hon. Dandutse sune; Manajan Gonar, Malam Ilyasu Umar, Alhaji Rabi’u Isah, Alhaji Atiku Muhammad Dukke, Malam Bara’u Yusuf, sai Majalisar Tsaro ta Karamar Hukumar Funtua.

A zaman, kamar yadda wadanda suka halarta suka tabbatar wa jaridun KATSINA CITY NEWS cewa, baki ya zo daya a kan cewa wannan hanyar ta fi shekaru 70 makiyaya da manoma na amfani da ita.

See also  Gidan zinare na marigayi Alhaji Mai Deribe a garin Maiduguri, Jahar Borno, Najeria.

Kazalika baki ya zo daya a kan cewa hanyar tana daga cikin hanyoyin da Hukuma ta yarda hanya ce domin amfanin manoma da makiyaya.

Baki ya zo daya cewa doka ta tabbatar da irin wannan hanyar ba a toshe ta, kuma ba a mayar da ita domin amfani wani mutum shi kadai. Amma duk da haka an samu rashin daidaito tsakani a kan yadda za a bude hanyar.

Bayan zaman, kwamitin ya ziyarci gonar, kuma ya je har dama din, ya kuma shiga cikin garin Dukke ya sake wani zaman a Funtua da Katsina. Sannan ya tsai da matsayar da aka rubuta wa Hon. Muntari Dandutse.
Wani dan kwamitin ya tabbatar wa da Wakilanmu cewa, sun rubuta rahoton sun mika wa gwamnatin Jiha, wanda a rahotonsu sun tabbatar cewa wannan hanyar, hanya ce ta amfani makiyaya da manoma, wadda bai kamata a toshe ta ba.

Kuma sun rubuta wa Alhaji Muntari Dandutse cewa toshe wannan hanyar kuskure ne, kuma ya kamata a bude ta don amfani manoma da makiyaya, kamar yadda take a tsare-tsaren zaman lafiya da kwanciyar hankali ga manoma da makiyaya.

Dan kwamitin ya tabbatar mana da wannan wasika ta bude hanya an isar da ita ga Muntari Dandutse ta hannun wakilansa, kuma sun ce sun isar da sakon. Sai dai har lokacin da muka yi magana da shi a 10/11/2021 ba a bude wannan hanyar ba.

A ranar Alhamis 11/11/2021 mun aika wa Hon. Dandutse sako ta wayar shi don jin nasa bahasin, amma bai ba da amsa ba. Mun sake maimaita sakon a ranar 20/11/2021, nan ma ba amsa. Mun sake maimaita tara masa sakon a ranar 1/12/2021, shi ma ba amsa.

Mun kira wayarsa a ranar Laraba 5/12/2021, ya dauka, muka gabatar masa da labarin da muke da shi, muna neman jin ta bakinsa, bayan ya gama jin bayaninmu, sai ya ce yana kan hanya, amma zai kira. Sai dai har zuwa rubuta rahoton nan bai kira ba.

Wakilanmu sun je garin na Dukke sun ga yadda mutane ke shan bakar wahala kafin su isa wajen sana’arsu da suke yi tun iyaye da kakanni. Sun bayyana mana cewa lokacin da gonar na hannun Marigayi Babajo, babu taimakon da ba ya yi masu. “Haka ma da tana hannun Marigayi Sani Idris Bagiwa ya taimaka mana. Ya taimaki ’ya’yanmu”, in ji su.

Suka ce yanzu su ba ta wani taimako suke ba, roko da kiran su kwara daya ne, a bude masu hanyar da suke bi zuwa sana’arsu tun iyaye da kakanni. “Wannan kiran ga Hon. Dandutse ne da kuma Gwamnan Katsina”, in ji mutanen garin Dukke.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
And all social media handles
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here