ZABEN KANANAN HUKUMOMI : ME YA SA MASARI YA CANZA

0

ZABEN KANANAN HUKUMOMI :
…….ME YA SA MASARI YA CANZA MATSAYARSA?

Suleiman Umar
@Katsina City News

A wani taron manema labarai da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya kira makwanni biyu da suka gabata, an yi masa tambaya a kan zaben kananan Hukumomi a Katsina, inda ya ba da amsar cewa gwamnatin Katsina za ta yi amfani da dokar Jiha ne wajen zaben, kuma za a yi zaben a kwatar farko ta shekarar da ake ciki ta 2022.

A kuma taron manema labaran da aka yi a Talata 11/1/2022, Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ta bayyana cewa, sun yi amfani da dokar zabe ta kasa, kuma sun ba da kwanaki 90 wanda zaben zai fada a kwata ta biyu ta shekarar 2022.

Binciken jaridun KATSINA CITY NEWS ya gano Shugaban Hukumar Zabe ta Jahar Katsina, Alhaji Ibrahim Bako ne ya gamsar da Gwamnan a kan a kauce wa fada wa rikicin kotu in aka yi amfani da dokar zabe ta Jiha wadda aka kafa tun zamanin tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Shehu Shema na mulki.

Alhaji Ibrahim Bako ya gabatar wa da Gwamnan Katsina, wasu hukuncin babbar kotun kasa guda biyu da suka jaddada amfani da dokar Hukumar Zabe ta kasa a wajen zaben kananan Hukumomi. Da kuma wasu hukunce-hukunce na soke zabe da aka yi a wasu Jihohi, wadanda aka yi zabe da dokar Jiha, amma bayan an yi kara kotu ta rusa zaben.

An kuma gabatar wa da Gwamnan cewa Jihohi 24 da suka yi zaben kananan Hukumomi duk da dokar zabe ta kasa suka yi amfani.

Bayan wannan tsarin mulkin kasa ya ce duk wata doka da ta yi karo da dokar kasa, wannan ta zama yasassa.

A bisa wadannan hujjojin Gwamnan ya ce, Kwamishinan Shari’a ya yi nazarinsu ya rubuto shawara, ya bi ya ba da shawarar cewa; “A zaben kananan Hukumomi na Jihar a yi amfani da dokar zabe ta kasa na bayar da kwanaki 90 domin gudanar da zabe.

Wannan shi ne ya sa Gwamnan Katsina ya canza shawara da kuma canza ranar zabe daga lokacin da ya shelanta a taron manema labarai zuwa ranar 11/4/2021, kamar yadda Hukumar Zaben ta Jiha ta tsara.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
And all social media platforms
07043777779 08137777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here