Bikin Naɗin Garkuwar Kabin Argungu Ya Ƙayatar Da Al’ummar Ƙasarnan

0

Bikin Naɗin Garkuwar Kabin Argungu Ya Ƙayatar Da Al’ummar Ƙasarnan

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Jama’a da dama ne suka halarci bikin naɗin sarautar Garkuwar Kabin Argungu, Injiniya Garba Haruna, wanda ya samu halartar manyan sarakuna, manyan jami’an gwamnati da manyan ƴan kasuwa, ƴan siyasa da attajirai.

Mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera CON shi ne ya yi wannan naɗi daga cikin naɗe naɗe da ya yi a fadar sa, albarkacin bikin cikarsa shekara 25 a karagar mulki, tare da ɗaurin auren ƴar sa, Hajiya Habiba Sama’ila Mera da sabon Garkuwar Kabin Argungu.

Sabon Garkuwar Kabin Argungun dai ya kasance shugaban Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna, wanda jama’a da dama suka shaide shi a matsayin mutum mai halayen ƙwarai da kowa ke farin ciki da shi, saboda yadda yake da kishin taimakon jama’a da samar wa matasan yankin Argungu ayyukan yi. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu ya ba shi wannan sarauta ta Garkuwar Kabin Argungu.

Sauran sarautun da aka naɗa sun haɗa har da Ganuwar Kabin Argungu, wanda aka bai wa shugaban Majalisar Dattijai ta ƙasa Sanata Ahmad Lawan. Sannan an kuma an yi wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar hawan daba, domin karrama waɗanda aka naɗa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here