MATSALAR FETUR A KATSINA

0

MATSALAR FETUR A KATSINA
@ katsina city news

Jaridun mu sun tabbatar da cewa daga nan zuwa litinin matsalar zata Rage a katsina.
An tabbatar mana cewa kamfanin matrix zai shigo da wasu motoci biyu zuwa lahadi.a sayar litinin
Wani jami in kamfanin A A rano yace zasu samar da mota daya a katsina zuwa lahadi,safiyar litinin a sayar.
Kamfanin Dan marna ya samar da motoci shidda a daren jumma a.za a fara sayar dasu yau asabar. Wasu motocin na kamfanin Danmarna zasu iso katsina zuwa litinin.
A jiya jumma a galan fetur a bayan fage ya haura naira dubu uku,har dubu hudu.
Amma samar da man da gidajen man Danmarna yayi safiyar yau asabar ya Sanya kasuwar ta bayan fage ta sauko kasa.
A Kewayen da mukayi a cikin katsina. Gidajen man Danmarna ke bada mai sai gidan man mega station dake garin dandagoro.sai gidan man dake kallon vision fm.
Katsina city news
Kamfanin Danmarna Wanda keda gidajen mai a duk fadin kasar nan.ya maida katsina cikin mafi muhimmaci wajen kai mansa in an dauko.kamar yadda binciken mu ya tabbatar.
Wannan dai matsalar ta duk kasar ce,Baki daya.wanda ta Sanya gamayyar jami an tsaro ke sa ido ga duk man da aka dauka.
Wannan ya Sanya ba yadda za ayi wani ya boye mai a halin da ake ciki.
@ www.katsinacitynews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here